'Dan Najeriya Ya Fallasa Bidiyoyin Tsoffin Yan Matansa 5 A Yanar Gizo, Ya Tada Kura

'Dan Najeriya Ya Fallasa Bidiyoyin Tsoffin Yan Matansa 5 A Yanar Gizo, Ya Tada Kura

  • Jama’a sun yi cece-kuce bayan wani matashi ya baje kolin tsoffin yan matansa biyar a soshiyal midiya
  • Matashin ya bayyana sunayen yan matan da bidiyoyinsu yayin da ya shiga wani sabon gasa na soshiyal midiya
  • Ya kuma bayyana abu daya da yayi kewa game da kowanne daga cikin yan matan da ya so a baya

Wani matashi ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya bayyana sunayen tsoffin yan matansa.

Matashin dan Najeriyan ya wallafa bidiyoyin kyawawan yan matan a kan TikTok yayin da ya shiga wani sabon gasa da ke bukatar mutum ya wallafa tsoffin yan matansa 5.

Yan mata
'Dan Najeriya Ya Fallasa Bidiyoyin Tsoffin Yan Matansa 5 A Yanar Gizo, Ya Tada Kura Hoto: TikTok/@olawealth64
Asali: UGC

Gasar na kuma bukatar wanda zai shige ta ya wallafa abu guda da yayi kewa game da tsoffin yan matan nasa.

Mutum na farko da ya wallafa wata budurwa ce mai suna Nancy wacce yace ya yi kewanta saboda iya soyayyarta. Sai Powesh wacce yayi kewa saboda ta iya gyara gado.

Kara karanta wannan

Borno: Matar Aure Ta Mutu Bayan Haihuwar Yan Uku A Sansanin Yan Gudun Hijira, Mijin Ya Bita Bayan 40

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran uku da ya wallafa sune Natasha, Mor Mor da Peace, yana mai cewa ya yi kewan kudi, ban hakuri da zantukan ban dariya daga kowannensu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Special❤️ ta ce:

“Kada wanda ya saka sunana a wannan gasar dai don da na kashe da dama.”

Oluwaseun ta yi martani:

"Idan wani ya sakani a wannan gasar shoponno zan kirawa mutum.”

Baby_vera❤️ ta ce:

“Kada wanda ya sakani a wannan wasar ni ba tsohuwar budurwar kowa bace.”

Duk Masu Zuwa Wurina Kudin Mahaifina Suke So Ba Ni Ba, Diyar Miloniya

A wani labarin, shahararriyar mai hada sautin kida ta Najeriya, Florence Otedola, wacce aka fi sani da Dj Cuppy, ta magantu game da dalilin da yasa har yanzu bata da tsayayyen namiji.

Cuppy ta bayyana cewa yawancin mazan da ke shigowa rayuwarta ba sonta suke yi da gaskiya ba illa sai don kudin mahaifinta, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Legas: Yadda Nayi Basaja, 'Dan Sanda Ya Nemi Cin Hanci Daga Wurina a Kan Titi, PPRO

Matashiyar wacce ta kasance diyar shahararren dan kasuwa nan kuma biloniya, Femi Otedola, ba ta ce bata damu da hakan ba illa dai ta mayar da hankalinta wajen ganin mafarkinta ya zama gaskiya da kuma samun ilimi don zama irin macen da take sha’awa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel