Atiku Ya Yi Magana Bayan Fallasar Wike, Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Ci Zabe A 2023
- Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya ce za a warware rikicin jam'iyyar nan ba da dadewa ba
- Atiku ya ce rikicin da ake yi a jam'iyyar na cikin gida wanda za a warware nan ba da dadewa ba
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a Akwa Ibom a ranar Juma'a, 23 ga watan Satumba, bayan fallasar da Wike ya yi yayin taron manema labarai
Akwa Ibom - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya tabbatarwa mutanen Akwa Ibom cewa za a warware rikicin cikin gida na jam'iyyar nan ba da dadewa ba.
Atiku ya bada tabbacin ne a ranar Juma'a yayin da ya ke yi wa mutane a filin wasanni na Godswill Akpabio yayin bikin cikar jihar shekaru 35 da kafuwa, rahoton Vanguard.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Atiku ya yi kira ga yan jihar su taimakawa PDP ta kwace mulki a kasa ta kuma cigaba da mulkar jihar.
PDP za ta warware matsalar ta ci zabukan 2023
Kalamansa:
"Na yi kira ga mutanen Akwa Ibom su cigaba da bawa gwamna goyon baya ya kammala cikin nasara. Na yi imanin da taimakon ku Fasto Umo Eno zai zama gwamna na gaba. Munyi imanin PDP za ta cigaba da mulki a Akwa Ibom yayin da jam'iyyar mu za ta dawo mulki a 2023.
"Eh, dole mu amince cewa muna fama da rikicin cikin gida, amma ku tabbatar cewa ba yakin dakushe karfin mu muke yi ba.
"Rashin jituwa ce ta siyasa kuma nan ba da dadewa ba, za mu warware komai kuma PDP za ta kara karfi har sai sun ci zabe a Fabrairun 2023 da izinin Allah."
Rikicin PDP: Su Dakatar Da Ni Idan Za Su Iya, Wike Ya Yi Wa PDP Barazana
A bangare guda, Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers, ya yi wa shugabannin PDP barazana ya ce su dakatar da shi kuma su shirya girben abin da zai biyo baya, The Punch ta rahoto.
Wike ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi a Port Harcourt, yana cewa jam'iyyar ta san abin da zai iya idan ta yi hakan.
Yana amsa tambayar da aka masa ne na cewa duba da irin yadda yan wasu jam'iyyun suka rika ziyartarsa ko hakan na iya zama cin amanar jam'iyyarsa.
Asali: Legit.ng