Manyan Illolin Shan Shisha Masu Barazana ga Lafiyar Matasa, Dr Maryam Mustapha

Manyan Illolin Shan Shisha Masu Barazana ga Lafiyar Matasa, Dr Maryam Mustapha

  • Dakta Maryam Mustapha ta bayyana illolin da shan shisha ke janyowa matasa wanda yanzu haka ya zama ruwan dare
  • Ta alakanta illolin shan shisha da kamuwa da cutar kansa ta huhu, ciki, hanji da sauransu bayan cutuka masu hatsari ga rayuwa
  • Har ila yau, shan shisha na iya kawo shanyewar bangaren jiki baya ga taba kwakwalwa da tunani da yake yi

Yanzu shan shisha ya zama tamkar yayi ko abun sha'awa ga jama;a kuma ya zama ruwan dare a cikin maatasa.

Mutane da yawa suna yin kuskuren cewa yana da sassauci a madadin shan taba sigari.

A cewar Cibiyar Kula da Cututtuka (CDC), a zahiri ba haka ba ne, kamar yadda binciken shisha da aka yi amfani da ita ya nuna cewa hayaki daga duka biyun yana dauke daiskar carbon-monoxide mai guba tare da sauran abubuwa da aka sani dake ƙara haɗarin cututtukan daji masu alaƙa da shan taba.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mai Garkuwa da Mutane dake Watsin Daloli a Soshiyal Midiya Yana Zubda Hawaye a Hannun 'Yan Sanda

Shan Shisha yana da illa kamar shan taba sigari, ko kuma fiye da hakan. An gano cewa hayakin da ke cikin shisha yana dauke da abubuwa masu cutarwa da yawa da ake samu a cikin hayakin sigari kamar nicotine, tar da sauransu.

Ko da yake wannan hayaƙin na iya wucewa ta magudanar tace ruwa a jiki, hayakin ba a tace shi a zahiri kuma abubuwan da ke cutarwa suna ci gaba da kasancewa ko da bayan sun wuce ta cikin ruwan jikin 'dan Adam.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A matsakaicin zaman shisha na sa'a daya, ana shakar hayaki kusan sau 100-200 idan aka kwatanta da sigari daya kusan sau 9 na adadin carbon-monoxide, kusan sau 1.5 ana shakar nicotine idan aka kwatanta da taba guda daya.

Shan shisha yana haifar da haɗari iri ɗaya da na shan taba sigari kamar kansar baki, kansar huhu, kansar ciki, cutar huhu, rage haihuwa da sauran su, kamar yadda Dakta Maryam Mustapha ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Budurwa ta shiga damuwa, ta hada kayataccen biki amma kawayenta suka ki hallara

A cewarta:

"Kwanan nan na ci karo da bayanin da kaina, wanda ke da matukar tada hankali. Shisha kanta na kunshe da abubuwa masu cutarwa kamar yadda taba sigari take.
"Har zuwa yanzu, wasu matasa sun daukar wa kansu suna kara abubuwa kamar tabar wiwi da sauran magunguna a cikin Shisha."
"Wannan na iya samun tasiri na jiki da na tunani gami da rashin tunani, ƙarancin tuna abubuwa a ƙwaƙwalwa da yanke shawara mara kyau. Wannan yana haifar da babban haɗari ga masu shaye-shaye da kuma al'umma baki daya.
"Na biyu, yana iya haifar da damuwa a kan wasu tsarin kamar tsarin garkuwar jiki, tsarin zuciya, tsarin numfashi da sauran su.
"Yana iya rinjayar tsarin jin tsoro wanda zai iya haifar da kamawa, bugun jini da wasu cututtuka na tunani. A cikin yanayin da ya wuce kima, yana iya zama haɗari ga rayuwa yayin da mutane ke iya suma, su kasa sarrafa hanyar numfashi."

Kara karanta wannan

Jerin Mutane 3 Da Suka Yi Fice Saboda Halitta Ta Musamman Da Suke Dauke Da Su

- Likita tace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng