Yan Bindiga Sun Sace Yan Sanda Da Tsakar Rana A Jihar Ogun
- Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun sace jami'an yan sandan Najeriya a karamar hukumar Ewekoro, Jihar Ogun
- Majiyoyi sun bayyana cewa yan sandan sun taho ne daga Legas zuwa Ogun don yin wani bincike amma maharan suka tare su a hanya da tsakar rana suka yi awon gaba da su
- Kakakin yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kuma ce jami'ansu sun fara farautan maharan don ceto wadanda aka sace
Jihar Ogun - Yan bindiga sun sace jami'an rundunar yan sanda uku a Wasinmi, karamar hukumar Ewekoro ta Jihar Ogun.
Daily Trust ta rahoto cewa an sace wadanda abin da ya faru da su ne da rana tsaka kuma sun ziyarci jihar Ogun ne daga Zone 2 Onikan Legas don bincike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ce yan sandan sun gabatar da kansu a ofishin yan sanda a Wasinmi kafin suka tafi inda za su yi aikin.
An sace yan sandan, da Sufeta Oladipo Olayemi, ke yi wa jagoranci ne misalin karfe 2.30 na rana.
Wakilin majiyar Legit.ng Hausa ya tattaro cewa wani direban motan haya da ya dauko yan sandan a motarsa ya sha da kyar.
Jami'an yan sanda na jihar karkashin DPO a Ewekoro sun fara farautan maharan da suka sace jami'an.
Kakakin yan sandan Jihar ya yi martani
Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da cewa mutanen amma ya ce 'dan sanda daya kawai aka sace'.
Ya ce:
"Muna bin sahun masu garkuwa da mutanen. Kana tunanin za mu yi shiru ne? Za mu kamo su mu kuma ceto wadanda abin ya shafa."
An Cafke Farfesan Da Ta Yi Wa 'Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' A Abuja, Yan Najeriya Sun Yi Martani
An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta
A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.
An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.
Asali: Legit.ng