2023: Jigon APC Ya Bayyana Adadin Kuri'un Da Tinubu Zai Samu Daga Yankin Yarbawa

2023: Jigon APC Ya Bayyana Adadin Kuri'un Da Tinubu Zai Samu Daga Yankin Yarbawa

  • Victor Olabimtan, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ondo ya bayyana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba zai gaza samun kashi 90 cikin 100 na kuri'un kudu maso yamma ba
  • Jigon na jam'iyyar APC mai mulki a kasa ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wa yan kungiyar goyon bayan Tinubu na BAT Vanguard a Akure, babban birnin jihar Osun
  • Olabimtan ya ce Tinubu dan su ne kuma yan Najeriya sun san zai kawo canjin alheri a kasar don haka dole su yi duk mai yiwuwa don ganin ya yi nasara

Akure - Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Hon. Victor Olabimtan ya ayyana cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu zai samu kuri'u kashi 90 cikin 100 a Kudu maso Yamma a 2023.

Kara karanta wannan

Tinubu Babban Kadarane, Gwamna Ganduje Ya Bayyana Kadan Daga Halayen Tinubu

Olabimtan, wanda shine shugaban kungiyar Bola Ahmed Tinubu Solidarity Vanguard ya ce hakan zai yi wu idan dukkan kungiyoyin goyon baya suka yi aikinsu yadda ya dace, rahoton The Nation.

Bola Ahmed Tinubu
Tinubu Zai Samu Kuri'u Kashi 90 Cikin 100 A Jihohin Kudu Maso Yamma, In Ji Olabimtan. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Olabimtan, yayin jawabinsa ga mambobin kungiyar a Akure, ya yi bayanin cewa kungiyarsu bata gasa da kowa amma aiki ta ke son a yi tare don ganin Tinubu ya yi nasara.

Ya ce yan Najeriya sun san cewa Tinubu zai kawo canji na alheri a kasar.

Tinubu zai samu kashi 90 cikin kuri'u a yankin yarbawa idan muka hada kai muka yi aiki tare - Olabimtan

Kalamansa:

"Muna bukatar shugaban kasa kamarsa. Mutumin da zai saka kafarsa a kasa ya tabbatar abubuwa sun tafi yadda ake so. Najeriya, karkashin Tinubu za ta gyaru.
"Na fi mayar da hankali kan Kudu maso yamma. Bola Ahmed Tinubu dan mu ne, dole mu yi duk mai yiwuwa don ganin ya yi nasara. Dole mu fita mu tattaro mutane mu tallafa masa.

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

"Inda muke bukatar gamsar da mutane, mu yi hakan. Inda muka bukatan bada hakuri, mu yi hakan. Yadda za mu yi aikin nan zai nuna makomar kasar Yarbawa. Idan aka yi aikin da shauki da zuciya daya, bana tsammanin Tinubu zai samu kasa da kuri'u 90 cikin 100 da za a kada."

Ba Buhari Bane Matsalar Najeriya, Ku Dena Dora Masa Laifi, In Ji Babban Malamin Addini

A wani rahoton, Malamin addini dan Najeriya mazaunin Birtaniya kuma babban fasto a cocin Faith Tabernacle, Apostle Alfred Williams, ya ce kada a dora wa Buhari laifi bisa matsalolin Najeriya.

Williams ya ce tsarin yadda Najeriya ta ke ne ke kawo cikas ga kyawawan niyya da Buhari ke da shi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya yi magana yayin ziyara da ya kai gidan talabijin na kasa, NTA, a Abeokuta, Jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164