‘Yan damfara Sun yi wa Asusun Bayin Allah Tas a Banki, Sun Sace Naira Miliyan 523
- Kwanakin baya, ‘yan damfara suka yi kwanaki uku a jere, suna cin karensu babu babbaka a Najeriya
- A tsakanin wannan lokaci aka nemi N523,337,100 daga asusun mutane, amma aka rasa inda suka shiga
- ‘Yan sanda sun ce an soma damke wadanda suka yi wannan danyen aiki domin ayi shari’a da su a kotu
Lagos - Wasu mutane da ake zargin ‘yan damfara ne, sun yi kwana uku suna ta’adi, har ta kai sun sace makudan kudi daga wasu bankunan Najeriya.
Daily Trust ta kawo rahoto a makon nan cewa a sanadiyyar kutsen da aka yi wa bankuna, ‘yan damfaran sun sulale da kudin da ya kai N523,337,100.
Kamar yadda rahoton ‘yan sanda ya tabbatar, an dauke wadannan kudi daga asusun abokan huldar bankin, aka yi ta aika da su zuwa wasu asusu dabam.
Kakakin sashen laifuffuka na musamman na rundunar ‘yan sanda da ke Ikoyi, a jihar Legas, SP Eyitayo Johnson ya fitar da jawabi a kan abin da ya faru.
Abin ya shafi asusun mutane da yawa
Eyitayo Johnson yake cewa ‘yan damfaran sun yi yawo da kudin daga asusu 18 da aka yi wa kutse, zuwa akawun akalla 225 da ake da su a bankuna 22.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mai magana da yawun jami’an tsaron yace an tafka damfarar ne a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu 2022, aka cigaba har zuwa tsakiyar daren 25 ga Afrilun.
Ba a yin bari, a dauke duka
Jami’in ya kara da cewa ‘yan sanda sun kama mutane biyu da ake zargi suna da hannu a laifin.
Pulse tace an iya karbo N160,287,071.47 daga cikin abin da aka dauke bayan an yi ta bincike a wasu bankuna da ake zargin kudin da aka sace sun shiga.
Bugu da kari, da zarar an karkare binciken da ake yi, kakakin ‘yan sandan yace za su gurfanar da mutanen da suka shiga hannu, domin ayi masa hukunci.
...Ya tsere da $120,000.00.
Ana haka sai Punch tace ‘yan sanda sun yi ram da wani Sikiru Olayinka mai kamfanin Excampo Nigeria Ltd, ana zarginsa da lakume $123,000.00.
Abin da ya faru shi ne an yi kuskuren aiko da Daloli a akawun din 'dan kasuwan, shi kuwa yana jin kudi sun shigo masu, sai ya ruga banki ya cire $120, 000.
An yi ta kokarin a karbe wadannan kudi, amma Olayinka ya ki bari ayi hakan.
Trump a kotu
Kuna da labari wata Lauya ‘yar jam’iyyar Democrat ta shigar da karar da za ta iya kawo cikas ga ‘takarar’ Donald Trump da Jam’iyyar Republican a 2024
Letitia James tayi karar Trump da iyalansa da wani babban jami’in kamfaninsa a kotun New York, tace an dade ana boye gaskiyar dukiyar shugaban.
Asali: Legit.ng