"Idan Katsina Za Ta Iya, Ondo Ma Za Ta Yi' - Akeredolu Zai Siya Wa Amotekun Bindiga Duk Da FG Bata Yarda Ba
- Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya ce zai bijire wa umurnin gwamnatin tarayya ya siya wa jami'an tsaron jiharsa bindiga
- Babban lauyan mai mukamin SAN ya ce idan har gwamnatin tarayya ta amince jami'an tsaron jihar Katsina su rike bindiga, bai ga dalilin da za a hana na jiharsa ba
- Hakan na zuwa ne yan makonni bayan gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom shima ya ce idan gwamnatin tarayya bata bashi izini ba zai nema daga mutanensa
Ondo - Rotimi Akeredolu, gwamnan Jihar Ondo, ya ce jiharsa za ta siyo wa jami'an hukumar tsaro da yankin yamma, Amotekun makamai, rahoton The Cable.
Babban lauyan mai mukamin SAN ya ce idan gwamnatin tarayya za ta kyalle jami'an tsaro a Katsina su dauki makami, ya kamata a bawa Amotekun wannan damar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Bidiyon da ke yawo ya nuna kwatankwancin hukumar tsaro ta Amotekun a Katsina, suna neman umurnin gwamnatin tarayya na mallakar makamai abi ne mai tattare da hatsar.
"Hana Amotekun abin da ta ke bukata na gaggawa, damar daukan bindigan kin amincewa da tsarin tarayya ne da muke nema a tabbatar.
"Idan Katsina za ta iya mallakawa jami'an tsaron makamai, inda suka nuna AK47 ya nuna muna kasa daya amma tsari daban-daban."
Ya cigaba da cewa:
"Hana Amotekun damar mallakar makamai na jefa kudu maso yamma cikin hatsari na mahara. Kuma wani mataki ne na lalata bangaren noma a yankin. Barazana ce ga rayuwa.
"Muna jadada cewa, ba za mu yarda da fifita wasu jihohi kan wasu ba. Gwamnatin Ondo saboda don sauke nauyin da doka ya dora mata za ta siyo makamai don kare mutanen jihar ta."
Wannan kalaman na Akeredolu na zuwa ne makonni bayan Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, ya ce idan gwamnati ta ki amince wa jami'an tsaron jiharsa su mallaki makamai, zai nemi izini daga mutanensa.
Gwamnatin tarayya ta ce hukumomin tsaron da jihohi suka kafa ba su da hurumin mallakar bindiga.
'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa
A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng