Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Ta'addan Boko Haram Kwanton Bauna, Sun Kashe Tsageru 7 A Borno
- 'Yan ta'addan Boko Haram na dibar kashinsu a hannu yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da karya lagonsu
- An kai farmaki kan wasu 'yan ta'addan Boko Haram, an kuma yi nasarar fatattakar da dama daga cikinsu
- Majiyar tsaro ta ce, wasu da dama daga 'yan ta'addan sun tsere, amma kuma sun samu munanan raunuka
Jere, jihar Borno - Jami'an sojojin Operation Hadin Kai sun tarfa tawagar 'yan ta'addan da ake zargin 'yan Boko Haram a karamar hukumar Jere ta jihar Borno, an kashe shida yayin da daya ya tsira da raunin harbin bindiga.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Kyamla na karamar hukumar, kuma an kwato wasu kayayyakin aikata ta'addanci daga hannun tsagerun.
Wata majiyar tsaro ta shaida cewa, jami'an sun samu bayanan sirri ne da ya kai ga ragargazar wadannan 'yan ta'adda.
A cewar majiyar:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Dakarun Operation Hadin Kai sun hallaka 'yan tada kayar baya bakwai a wani farmaki, wasu da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga a kauyen Kayamka."
Kwararre kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya yi bayani kan yadda lamarin ya faru, ya ce wadanda aka kashen 'yan ta'addan Boko Haram ne da ke tserewa ragargazar jami'an tsaro.
An naqalto cewa, dakarun bataliya ta 73 da hadin gwiwar dakarun hadaka na CJTF ne suka kai wannan farmaki.
Majiyoyi daga yankin kuwa sun ce, 'yan ta'addan kan shigo yankin lokaci zuwa lokaci domin aikata ta'addancinsu kan manoma tare da sace mazauna a wasu lokutan.
Makama ya ce, a yanzu dai jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da matsa lamba wajen ragargazar 'yan ta'adda da masu taimaka musu a yankunan Arewa maso Gabas.
Hakazalika, ya ce hukumomin tsaron na yabawa irin ayyukan da sojoji da sauran jami'an tsaro ke yi a Arewa maso Gabas.
Mutanen Kauye da Ke Shirin Tserewa Harin ’Yan Bindiga Sun Nutse a Kogi a Abuja
A wani labarin, mutum biyar; maza hudu da wata matar aure sun nuste a garin tserewa harin 'yan bindiga a kauyen Chakumi a unguwar Gurdi ta Abaji a Abuja.
Rahoton Daily Trust ya ce, Chakumi gari ne mai makwabtaka da kauyen Daku mai hade da kogin Gurara a unguwar Dobi ta Gwagwalada a birnin na Abuja.
Mai garin Chakumi, Mohammed Magaji ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce hakan ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a ranar Laraba 21 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng