Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Gidan Maitama Sule Cibiyar Demokradiyya

Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Gidan Maitama Sule Cibiyar Demokradiyya

  • Gwamnatin Jihar Kano za ta mayar da gidan marigayi Dr Yusuf Maitama Sule zuwa gidan tarihi da cibiyar demokradiyya
  • Kwamishinan Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ne ya bada wannan sanarwar a ranar Laraba a Kano
  • Garba ya ce gwamnatin na Kano za ta kashe kudi kimanin Naira miliyan 621 wurin aikin da ake fatan zai zama mai amfani ga tarihi da ilimi a kasa

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta siya gidan marigayi Dr Yusuf Maimata-Sule, tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, UN, don gina cibiyar Demokradiyya da Gidan Tarihi, rahoton NAN.

Muhammad Garba, kwamishinan labarai na Kano ya bayyana hakan cikin wata sanarwa daya fitar yana mai cewa an dauki matakin ne don inganta demokradiyya da gwamnati mai kyau a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu Babban Kadarane, Gwamna Ganduje Ya Bayyana Kadan Daga Halayen Tinubu

Maitama Sule
Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Gidan Maitama Sule Cibiyar Demokradiyya. Hoto: @GuardianNG.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce tuni an fara aikin ginin a tsohon gidan da tsohon dakin karatu na cibiyar Birtaniya da ke kan hanyar Fadar Sarki a birnin na Kano.

Mr Garba ya ce aikin zai ci kudi kimanin Naira miliyan 621 kuma a mataki biyu za a yi, na farko shine gidan kayan tarihi sai cibiyan demokradiyya.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta fara aikin ne saboda muhimmancin tattalin kayan tarihi da al'adan mutanen Kano da kuma ayyukan bincike da masu yawon bude ido.

Mr Garba, ya ce cibiyar za ta rika bada horaswa, ajiye takardu da zamantar da tarihin mutanen Kano.

Kwamishinan ya kuma ce aikin zai bada damar hadin gwiwa tsare da cibiyoyin ilimi da wasu kungiyoyin na cikin kasa da kasashen waje don bincike.

Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Rade-radin Siyar da Kotunan Shari'ar Jihar

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Kama Ƴan Ta'addan Da Suka Sace Mahaifiyar Sanatan APC a Kano Da Kuma Kashe Jami'an Tasaro

A wani rahoton, kwamishinan shari'a na jihar Kano, Musa Abdullahi-Lawan, ya ce babu wani shirin da gwamnatin jihar take yi na siyar da kotunan shari'a a jihar.

Abdullahi-Lawan, shugaban kwamitin tattaunawa kan kadarorin gwamnati, ya sanar da hakan a Kano a ranar Laraba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Wasu daga cikin lauyoyin jihar Kano kamar su Sanusi Umar, Usman Imam da Bello Basi sun tunkari babbar kotun Kano wurin neman a dakatar da gwamnatin jihar daga gina wa da siyar da farfajiyar kotuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164