Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Rade-radin Siyar da Kotunan Shari'ar Jihar

Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Rade-radin Siyar da Kotunan Shari'ar Jihar

  • Gwamnatin ta musanta zarginta da ake yi da siyar da wasu kotunan shari'ar Musulunci dake fadin jihar Kano
  • Kamar yadda kwamishinan shari'a na jihar Kano, Musa Abdullahi-Lawan, yace sauyawa kotunan wurin zama aka yi amma duk da dalili
  • Wasu lauyoyi uku sun maka gwamnatin Kano a kotu kan zargin siyar da kotunan Gidan Maitatsine, 'Yan Alluna da sauransu

Kano - Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Musa Abdullahi-Lawan, yace babu wani shirin da gwamnatin jihar take yi na siyar da kotunan shari'a a jihar.

Abdullahi-Lawan, shugaban kwamitin tattaunawa kan kadarorin gwamnati, ya sanar da hakan a Kano a ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto.

Gudumar Kotu
Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Rade-radin Siyar da Kotunan Shari'ar Jihar. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wasu daga cikin lauyoyin jihar Kano kamar su Sanusi Umar, Usman Imam da Bello Basi sun tunkari babbar kotun Kano wurin neman a dakatar da gwamnatin jihar daga ginawa da siyar da farfajiyar kotuna.

Kara karanta wannan

FG da ASUU: Kotu ta Dage Sauraron Shari'a, Ta Saka Sabuwa Ranar Zama

Kotunan da hakan ta shafa sun hada da babbar kotun shari'a ta Gidan Maitatsin, Yan Awaki; Babbar kotun shari'a Yan Alluna; Babbar kotun shari'a ta Shahuci da babbar kotun shari'a ta Goron Dutse.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran sun hada da kotun shari'a ta Kasuwar Kurmi da babbar kotun shari'a ta Filin Hockey.

Abdullahi yace:

"Ikirarin da masu kai kara suka yi na bogi ne, bashi da tushe kuma na siyasa ne sannan rashin fahimta ne.
”Gwamnatin jihar bata da shirin canza kotunan Shari'a na Goron Dutse da ta filin Hockey a Hausawa wuraren zama."
"Hukuncin gwamnatin jihar na sauyawa babbar kotun shari'a ta Yan Awaki wurin zama ya biyo bayan mamaye ginin kotun da tashar motar Kofar Wambai da kasuwa suka yi.
“Bai dace kotu ta kasance a wurin da akwai hayaniya ba tare da wasu abubuwan dauke hankali wanda ka iya jan hankalin alkali, jami'an jotu da wadanda ake shari'a.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Sanda Sun Damke Jiga-jigan PDP 2 Kan Zargin Zugawa Abacha Karya

"Kotu tana bukatar wurin da zai kasance ba mai barazana ga shari'a. An mayar da kotun 'yan awaki kan titin BUK New Site inda aka hada da wasu manyan kotuna uku da za a kammala gininsu a watan Satumban 2022."

- Yace.

Alkali Ya Aika Matashi Gidan Yari Bayan Ya Watsawa 'Yar Sanda Najasa

A wani labari na daban, wata kotun gargajiya mai daraja ta daya dake Ibadan jihar Oyo, a ranar Litinin ta yankewa matashi mai shekaru 23 mai suna Abayomi Damilare hukuncin zaman gidan maza na wata shida bayan ya watsawa ‘yar sanda kashi.

Alkalin kotun ta yankewa matashin wannan hukuncin bayan ya amsa laifinsa tare da shaidu gamsassu da aka mikawa kotun.

Akintayo a takaice ta yi shari’a tare da yankewa matashin hukuncin wata shida a gidan yari da aiki mai wahala.

Alkalin ta kwatanta wanda ta yankewa hukuncin da mai laifin da ba zai taba tuba ba, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sakamakon Binciken da Muka Gudanar Kan Tukur Mamu Yana Da Daure Kai, DSS

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel