Hotunan Wani Jami'in Sojan Bogi Da NSCDC Ta Kama a Nasarawa Yana Damfarar Mutane
- Dubun wani mutum mai yi wa dakarun sojojin Najeriya sojan gona a jihar Nasarawa yana karban kudi hannun jama'a a cika
- Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ne a Nasarawa suka kama Moses Ayaka, dan shekara 32 a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa
- Ayaka, a yayin da ake masa tambayoyi bayan kama shi ya amsa cewa ya damfari mutane kudin da ya tasanma N440,000 a jihar
Jihar Nasarawa - Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC sun yi nasarar kama wani sojan bogi mai shekaru 32 a Jihar Nasarawa.
The Punch ta rahoto cewa an kama wanda ake zargin, Moses Ayaka, a karamar hukumar Lafia, babban birnin jihar.
Kafin kama shi, wanda ake zargin, an ce ya dade yana damfarar mazauna garin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayaka da kansa ya bayyana cewa ya damfari fiye da mutane 22 ya kwace musu kudi da ya kai N440,000.
Rundunar ta ce za a mika shi hannun yan sanda domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da shi a gaba kotu ya girbi abin da ya shuka.
Kano: Saboda Budurwa, Asirin Wani Da Sojan Bogi Ya Tonu, An Kama Shi Da Bindiga Da Harsashi
A wani rahoto mai kama da wannan, An kama wani mutum da ake zargi, da ba a riga an bayyana sunansa ba a Kano dauke da bindiga da albursai da kayan sojoji a Kano, Daily Trust ta rahoto.
An gano cewa wanda ake zargin yana basaja ne a matsayin soja, da suna M.A. Ibrahim, kuma yana kwatar kudade hannun mutane kan hanyar BUK road a jihar.
Shaidan gani da ido wanda ya nemi a boye sunansa ya ce wanda ake zargin yana zama ne a unguwar Danbare kusa da BUK, kuma ya rika fada wa mutane cewa shi kyafin ne a rundunar sojojin Najeriya.
Asali: Legit.ng