Yayin da Ake Jiran Bayani, Sanatoci Sun Yi Shiru Kan Batun Tsige Shugaba Buhari
- Majalisar dattawa ta yi tsit game da batun tsige Buhari, duk da a baya wasu sanatoci sun ba shugaban wa'adin kawo karshen matsalar tsaro
- Majalisar dattawa ta yi hutun wani dan lokaci, inda ta dawo ci gaba da zaman majalisa a cikin makon nan
- 'Yan Najeriya na ci gaba da shiga damuwa kasancewar yadda batun tsaro ke kara zama mummuna a kwanakin nan
FCT, Abuja - Sanatoci a Najeriya sun ci gaba da zaman majalisa a ranar Talata 20 ga watan Satumba, amma sun yi shuru game da batun kawo karshen zaman Shugaba Muhammadu Buhari a kujerar mulkin Najeriya.
Idan baku manta ba, sanatoci daga jam'iyyun adawa daban-daban sun tada batun ko dai Buhari ya gyara lamarin tsaron Najeriya ko kuma su tsge shi, Punch ta ruwaito.
Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin ASUU da majalisa, za a kai batu gaban Buhari kafin a koma makaranta
Majalisar ta ba Buhari wa'adin makwanni shida ya tabbatar ya kawo karshen matsalar rashin tsaro, kana kasa ta zauna lafiya.
Bayan an dawo zaman majalisa, babu sanatan da ya kawo batun a zauren majalisa, kuma babu wanda ya yi magana da manema labarai kan batun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Madadin magana game da tsige Buhari, Ahmad Lawan ya dago batun tsaro inda yace:
"'Yan uwa abokan aiki, kafin mu tafi hutu, majalisar sanatoci ta nuna matukar damuwa game da lamarin tsaron kasar nan. We yi tattaunawa game da kalubalancin tsaro a kasar nan."
Hakazalika, ya bayyana cewa, majalisar ta zauna da masu ruwa da tsaki a fannin tsaron Najeriya, kuma an tattauna don nemo mafita mai daurewa ga matsalolin tsaro.
Ana samun nasara a fannin tsaro
Da yake karin haske, ya ce hukumomin tsaro suna samun nasarar shawo kan matsalar tsaro, inda ya ba da tabbacin cewa za a samu ci gaba mai daurewa, rahoton kafar labarai ta ReubenAbati.
"Daga bayanan da suka tabbata, hukumomin tsaronmu na samun nasara sosai kuma lamarin na samun sauki."
A bangare guda, ya ce majalisar dattawa za ta ci gaba da kai komo da tattaunawa da hukumomin tsaro domin sanin halin da ake ciki.
A wani labarin, wa'adin makwanni shida da aka dibarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya warware matsalolin tsaron Najeriya sun shude, har yanzu abubuwa basu kankama ba.
A cewar rahoton jaridar The Guardian, majalisar dokokin Najeriya za ta sake zama a ranar Talata mai zuwa, 20 ga watan Satumba don sake duba batun tsige shugaban.
Idan baku manta ba, rahotanni sun karade Najeriya a ranar 27 ga watan Yuli cewa, majalisar dattawa ta dago batun tsige Buhari saboda ta'azzarar lamurran tsaro.
Asali: Legit.ng