Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Yafewa Su Dangote Harajin Naira Tiriliyan 16 a Shekara 3
- Gwamnatin tarayya ta yafewa wasu kamfanoni biyan haraji tsakanin 2019 da 2021 domin bunkasa tattalin arziki
- Ana yin haka ne domin a kwadaito manyan kamfanoni su zuba hannun jari a Najeriya, ta yadda za a samu ayyuka
- African Foundries Ltd, Royal Pacific Group Ltd, Kunoch Hotels Princess Medi Clinics Nigeria sun amfana da tsarin
Abuja - Bayanan da aka samu daga shafin ofishin kasafin kudin Najeriya, ya nuna cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta yafewa wasu kamfanoni haraji.
Jaridar Punch tace tsakanin shekarar 2019 zuwa shekarar 2021, gwamnatin tarayya tayi afuwar harajin Naira Tiriliyan 16.76 ga wasu kamfanonin kasar nan.
Kamfanonin da suka ci moriyar wannan sauki da aka yi sun hada da Dangote, Lafarge, Honeywell.
Akalla kamfanoni 46 suka ci ribar tsare-tsaren afuwar haraji da kudin biyan shigo da kaya da gwamnati ta rika yi wa wasu 'yan kasuwa har zuwa karshen 2021.
Kamfanoni na neman sauki
Sahara Reporters tace a tsawon lokacin da wadannan kamfanoni suka huta da biyan haraji, akwai kamfanoni 186 da suka nemi irin damar, ba su kai ga dacewa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A irin wannan tsari, gwamnatin tarayya tana yafe karbar harajin kudin shiga, harajin VAT, harajin fetur da kudin da kwastam ke karba wajen shigo da kaya.
An yafe N4.2tr a 2019
Rahoton TES ya nuna a shekarar 2019, gwamnatin Muhammadu Buhari ta hakura da har Naira tiriliyan 4.2 daga harajin CIT da VAT da ake biyawa kayan masarufi.
Abin da ya kamata ya shiga asusun gwamnatin Najeriya daga harajin CIT ya haura Naira tiriliyan 1.1, sannan ya kamata a karbi VAT na Naira tiriliyan 3.1 a lokacin.
Rashin alkaluman kudin da ake samu daga harajin kudin shiga, PPT, da kudin kwatsam ya sa ba a iya tantance abin da aka rasa ba, da adadin ya zarce haka.
N5.8tr a 2020, kusan N7tr a 2021
A shekarar 2020, rahoton ya nuna afuwar da gwamnati tayi ya karu zuwa N5.8tr. Harajin VAT ne ya ci N4.3tr, yayin da CIT da PPT suka ci N457bn da N307bn.
An kuma yafewa kamfanonin nan biyan N780bn da ya kamata su tafi asusun hukumar kwatsam.
Zuwa shekarar 2021, afuwar da aka yi ta kai ta N6.79tn. VAT ya ci N3.87tn, CIT ya ci N548.40bn, N337.70bn daga PPT. Ragowar ne abin ya kamata kwastam su karba.
Buba Marwa yana kokari
An samu rahoto Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jinjina na musamman ga shugaban hukumar NDLEA watau Buba Murwa kan irin kokarin da yake yi.
Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar da jawabi, yana cewa Buhari yana alfahari da aikin Marwa bayan an kama hodar iblis na kusan N200bn a Legas.
Asali: Legit.ng