Dole a Binciki Sule Lamido da ‘Ya ‘yansa Kan Zargin Satar Naira Miliyan 712 inji Kotu
- Alhaji Sule Lamido bai iya dakatar da Hukumar EFCC daga binciken da take yi wa shi da wasunsa ba
- Lauyan tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya kalubalanci EFCC a zargin badakalar fiye da N700m
- Alkali tace wajibi ne wadanda ake tuhuma su kare kansu daga laifin da Hukumar EFCC jefa masu
Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta yanke hukunci cewa dole Sule Lamido da wadanda ake tuhuma su amsa zargin da ake yi masu.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta wallafa labarin yadda ta kaya a zaman kotu a ranar Litinin a shafinta a Facebook.
A jiya Alkalin kotun tarayya, Ijeoma Ojukwu tayi watsi da rokon da Lauyan Sule Lamido yake yi a zargin da ake yi masu na satar kudi, Naira miliyan 712.
Bayan an gama kiran shaidu da suka fadi abin da suka sani, Lauyan da ya tsayawa tsohon gwamnan ya yi ikirarin masu tuhuma ba su iya kawo hujjoji ba.
Amma Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ba ta gamsu da wannan ba, ta yarda da korafin Lauyan EFCC watau Chile Okoroma da yace Sule suna da kashi a gindi.
Su wa ake tuhuma da laifi?
Sauran wadanda ake tuhuma da laifin satar N712,008,035 tare da jigon na PDP sun hada da ‘ya ‘yansa biyu - Aminu Sule Lamido da Mustapha Sule Lamido.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana kuma zargin abokin kasuwancin tsohon Ministan harkokin wajen, Aminu Wada Abubakar.
Kamfanonin da EFCC ta hada a shari’ar su ne: Bamaina Company Nig. Ltd., Bamaina Aluminium Ltd, Speeds Intl Ltd sai Batholomew Darlignton Agoha.
Mai magana da yawun EFCC a Najeriya, Wilson Uwujaren yace Alkali Ojukwu ta umarci Sule ya shirya kare kan shi daga ranar 8 ga watan Nuwamba.
Shari'ar EFCC da Sule Lamido
Zargin da ake yi wa fitaccen ‘dan siyasar shi ne ya dauki kudi daga baitul-malin jihar Jigawa a lokacin yana gwamna tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta fitar a rahotonta, tun a 2015 aka soma shari’ar a gaban Evelyn Anyadike, daga baya aka dawo wajen Ojukwu.
Asali: Legit.ng