FG da ASUU: Kotu ta Dage Sauraron Shari'a, Ta Saka Sabuwa Ranar Zama

FG da ASUU: Kotu ta Dage Sauraron Shari'a, Ta Saka Sabuwa Ranar Zama

  • Kotun masana'antu dake zama a Abuja ta dage sauraron shari'ar ASUU da gwamnatin tarayya zuwa ranar 16 ga Satumba
  • Mai shari'a Polycarp Hamman, yace ya yi hakan ne domin gwamnatin tarayya ta samu damar mika dukkan takardun da suka dace a gaban kotun
  • Gwamnatin tarayya dai ta maka ASUU a gaban kotun ne da bukatar a tirsasa malaman su komai aiki yayin da ake sasanci

FCT, Abuja - Kotun masana'antu a ranar Litinin ta dage sauararon sharia'a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU, zuwa ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa.iy

Mai shari'a Polycarp Hamman ya dage sauraron shari'ar ne saboda a bai wa gwamnatin tarayya mika dukkan takardun da suka dace don karar, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

FG da ASUU
FG da ASUU: Kotu ta Dage Sauraron Shari'a, Ta Saka Sabuwa Ranar Zama
Asali: UGC

Gwamnatin tarayya ta garzaya gaban kotun masa'antu ta kasa dake zama a Abuja inda take bukatar a umarci kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'i, ASUU, da su koma bakin aikinsu a yayin da ake kokarin shawo kan rashin jituwar dake tsakaninsu.

A wata takardar da shugaban yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar kwadago da aikin yi, Olajide Oshundun ya fitar, yace a ranar 8 ga watan Satumba ne ministan kwadago ya aike da lamarin gaban magatakardan kotun masana'antu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

ASUU ta fada yajin aikin sati hudu a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kuma ta cigaba duk da tattaunawar da take da gwamnatin ba a samun wata matsaya.

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

A wani labari na daban, ministan kwadago da daukar ma’aikata, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar maka kungiyar malaman jami’a ta ASUU a kotu saboda an kasa cimma matsaya daya tsakanin bangarorin biyu.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: FG Na Iya Sauya Hukunci, Zata Biya Malamai Albashinsu da ta Rike

Jaridar The Sun ta rahoto cewa za a fara sauraron shari'ar ne a ranar Litinin, 12 ga watan Satumba.

Batun zuwa kotun ya taso ne yan kwanaki bayan gwamnatin tarayya ta sanar da yiwa malaman jami’ar karin albashi da kuma alkawarin sama masu naira biliyan 150 a cikin kasafin kudin 2023 a matsayin kudaden farfado da jami’o’in gwamnatin tarayya, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel