Hukumar 'Yan Sanda: Idan Dan Sanda Ya Kafta Maka Mari, Ya Daki Banza Matukar Yana Sanye Da Inifam

Hukumar 'Yan Sanda: Idan Dan Sanda Ya Kafta Maka Mari, Ya Daki Banza Matukar Yana Sanye Da Inifam

  • Kakakin rundunar yan sanda ta kasa, ya bayyana cewa mutum bai da ikon ramawa koda ace dan sanda ya maresa idan dai har yana sanye da inifam
  • Olumuyiwa Adejobi, ya ce abun da ya kamata mutum yayi shine ya kai kara gaban hukumar doka don a tsawatar masa
  • Mai magana da yawun yan sandan ya ce cin mutuncin jami'in dan sanda da ke sanye da kayan aiki tamkar cin mutuncin Najeriya

Kakakin rundunar yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa idan da jami’in dan sanda zai mari wani dan farin hula, mai shi bai da damar ramawa.

Adejobi, wanda ya je shafinsa na Twitter don bayyana hakan, ya shawarci duk wanda irin haka ta cika da shi da ya shigar da kara a gaban hukumar doka.

Olumuyiwa Adejobi
Kakakin Yan Sanda Ga Yan Najeriya: Baku Da Yancin Ramawa Idan Dan Sanda Sanye Da Inifam Ya Mare Ku Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga wani bidiyo da ya yadu na wani mutumi da ke jan bindiga da dan sanda a yayin wata zazzafar muhawara.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas

Kakakin yan sandan ya kuma bayyana cewa idan wani ya ci zarafin jami’in dan sanda da ke sanye da kayan aiki, kamata yayi a kalli hakan a matsayin cin mutuncin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Koda jami’in dan sanda da ke sanye da inifam ya mari dan farin hula, dan farin hulan bai da yancin ramawa. Bugud da kari, idan yana sanye da inifam, hakan rashin mutuntawa ne ga Najeriya a daki wani jami’I da ke sanye da inifam. Wannan cin mutuncin b aga jami’in dan sanda bane illa ga kasarmu kuma laifi ne kamar yadda yake a tanadin dokokinmu.
“Saboda haka, ba batun abun da jami’in dan sandan yayi da ya kai ga haka bane, sai dai martanin yan farin hula wadanda ke cin zarafin yan sanda. Idan dan sanda ya ci zarafin dan farin hula, sai ka kai kara kuma za a dauki mataki don tsawatar masa, amma ba wai ka dauki doka a hannunka ba.”

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Rashin Tsaro: Amotekun Za Ta Yaki Yan Bindiga Da Kudan Zuma Da Macizai

A wani labari na daban, Shugaban hukumar tsaro na Amotekun reshen jihar Oyo, Janar Kunle Togun (mai ritaya) ya yi barazanar amfani da kudan zuma da macizai masu dafi wajen farmakan yan bindiga da ke addaban jihar da yankin.

Togun ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kungiyar ODCF da aka gudanar a karshen mako a dakin taro na Otu da ke karamar hukumar Itesiwaju na jihar.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bar jami’an hukumar su yi amfani da bindigar AK 47 da sauran makamai wajen yaki da ta’addanci a jihohin da ke kudu maso yammacin kasar, jaridar Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel