Rashin Tsaro: Amotekun Za Ta Yaki Yan Bindiga Da Kudan Zuma Da Macizai

Rashin Tsaro: Amotekun Za Ta Yaki Yan Bindiga Da Kudan Zuma Da Macizai

  • Janar Kunle Togun (mai ritaya) ta yi barazanar amfani da kudan zuma da macizai masu dafi wajen yaki da yan bindiga
  • Janar din ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da bar jami’an Amotekun su yi amfani da bindigar AK 47
  • Togun ya kuma bayyana cewa jihar Oyo ce ta daya a wuraren da yan bindigar waje ke hari saboda tana da yalwataccen fili

Oyo - Shugaban hukumar tsaro na Amotekun reshen jihar Oyo, Janar Kunle Togun (mai ritaya) ya yi barazanar amfani da kudan zuma da macizai masu dafi wajen farmakan yan bindiga da ke addaban jihar da yankin.

Togun ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kungiyar ODCF da aka gudanar a karshen mako a dakin taro na Otu da ke karamar hukumar Itesiwaju na jihar.

Kara karanta wannan

Ci gaba: Fasihi ya jawo cece-kuce yayin da ya kirkiri 'Wheelbarrow' mai amfani da inji

Amotekun
Rashin Tsaro: Amotekun Za Ta Yaki Yan Bindiga Da Kudan Zuma Da Macizai Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bar jami’an hukumar su yi amfani da bindigar AK 47 da sauran makamai wajen yaki da ta’addanci a jihohin da ke kudu maso yammacin kasar, jaridar Leadership ta rahoto.

Ya bayyana cewa jihar Ogun ce ta daya da yan bindigar waje ke hari saboda girman filinta da ke kusa da iyakokin kasahen waje da kuma dazuzzuka inda za su iya boyewa da farmakar mutanen, musamman a yankin Oke-Ogun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Togun ya ce:

“A lokacin da duniya ke fama da annobar korona, an bar wadannan mutane sun shigo Najeriya da kowani lungu na kasar da suke burin zuwa ba tare da tsangwama ba, shugaba Buhari ne uban goyonsu kuma duk mun sani.
“Wadannan mutane sun zo Oke-Ogun a cike tireloli kuma wasu daga cikin sarakunanmu na gargajiya sun yarda da wannan a yankinsu duk da cewar mutane sun dauki hotuna da bidiyoyi wanda suka watsa a soshiyal midiya, ba za mu daina magana kan haka ba.

Kara karanta wannan

Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu

“Don dorewar zaman lafiya da korar wadanan yan bindiga za mu yanke shawarar amfani da kudajen zuma da macizai masu dafi, na je har yankin ‘Ibariba’ don ganin wani babban maharbi kan haka, wannan zai iya sauya mahangar yaki a duniya maimakon makami, kawai muyi amfani da namun daji kowa ya huta.”

Yan Sanda Sun Kama Isiyaku Babangida, Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara Da Ake Nema Ruwa A Jallo

A wani labarin, mun ji cewa rundunar yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun kama wani Isiyaku Babangida, kasurgumin dan bindiga da ake nema ruwa a jallo.

Kakakin yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ne ya sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, jaridar The Cable ta rahoto.

A cewar Shehu, an kama Babangida ne a yayin wani aiki da jami’an tsaro suka gudanar a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke jihar.

Kara karanta wannan

Hotunan Ummi, Kyakkyawar Budurwar Da Ta Rasa Ranta A Farmakin Da Yan Bindiga Suka Kai Bankunan Kogi

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel