Wasu Sun Farmaki Coci, Sun Lakadawa Fasto Duka Yayin da Yake Wa’azin Ranar Lahadi
- Wasu mutanen da ba a gane ko su wanene ba sun farmaki coci a jihar Filato, sun yiwa fasto bulala
- Masu bauta a cocin sun shiga tsoro, lamarin da ya kai ga lalata abubuwa da dama a cocin dake kauyen Shikal
- Ana yawan samun rikicin addini a jihar Filato, wannan yasa jihar ta yi kaurin suna wajen samun rikici-rikice
Lantang, jihar Filato - Wani coci a kauyen Shikal na karamar hukumar Lantang ta Kudu ya fuskanci farmakin wasu mutanen da suka badda kamanni da shigar dodanni a ranar Asabar 17 ga watan Satumba.
Rahoton da muke samu daga jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, wadanda suka farmaki cocin sun yiwa masu bauta da fastonsu bulala tilis.
Baya ga cin zarafin fasto da mabiyansa tare da watsa kowa dake cikin cocin, an ce sun kuma yi kaca-kaca da kayan kidan cocin da sauran abubuwa masu amfani.
Budurwa Mai Shekaru 92 da Bata Taba Soyayya ba ko Aure Ta Bayyana Babbar Nadamarta a Bidiyo Mai Taba Zuciya
An ce mutanen sun farmaki cocin ne a daidai lokacin da mabiya addinin kirista ke gabatar da bauta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani shaidan gani da ido ya ce, masu bautan sun yi matukar tsorata, kuma basu yi wata-wata ba illa gudu, kuma basu dauki wani mataki ba face tattara sauran abubuwan da aka lalata.
Ya kuma bayyana cewa, dukkan mambobin cocin sun tsere ba tare da rauni ba, rahoton Daily Sun.
Ya zuwa yanzu dai dattawan yankin na yin mai yiwuwa domin shawo kan lamarin tare da kokarin wanzar da zaman lafiya.
Majiya ta tuntubi kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen karamar hukumar da lamarin ya faru, amma bata samu bayani daga gare ta ba.
'Yan Sanda Sun Fatattaki 'Yan a Mutun Peter Obi da Suka Fara Gangami a Jihar Ebonyi
A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta fatattaki dandazon jama'ar da suka taru a Abakaliki a dandazon mutum miliyan magoya bayan dan takarar shugaban kasan LP, Peter Obi.
Rahoton The Nation ya ce, masoya Obi sun taru ne a Pastoral Centre dake Abakaliki, inda 'yan sanda suka fatattake su da barkonon tsohuwa.
An ce lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin Old Enugu a birnin na Abakaliki a yau Asabar 17 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng