Budurwa Mai Shekaru 92 da Bata Taba Soyayya ba ko Aure Ta Bayyana Babbar Nadamarta a Bidiyo Mai Taba Zuciya

Budurwa Mai Shekaru 92 da Bata Taba Soyayya ba ko Aure Ta Bayyana Babbar Nadamarta a Bidiyo Mai Taba Zuciya

  • Xavelin 'yar kasar Congo mai shekaru 92 wacce bata taba soyayya ko kasancewa da namiji ba tace tana takaicin kadaicin da take ciki
  • Tsohuwar mai kwazo tace shekarunta kawai sun tafi babu namijin da ya taba zuwa wurinta domin neman aurenta
  • Wasu daga cikin danginta sun sakankance cewa akwai yuwuwar asiri ko maita a cikin lamarin da yasa har yanzu bata yi aure ba

A shekaru 92 a duniya, Xavelin 'yar asalin kasar Congo tsohuwa ce dake zama cikin kadaici kuma babban nadamar da tayi a rayuwa shi ne rashin kula samari har ta kai ga aure.

Tsohuwar Budurwa
Budurwa Mai Shekaru 92 da Bata Taba Soyayya ba ko Aure Tayi Bayyana Babbar Nadamarta a Bidiyo Mai Taba Zuciya. Hoto daga Afri Max
Asali: UGC

A gidansu Xaveline, su 14 ne

Tsohuwar budurwar sun kasance su 14 ne gidansu kuma dukkan sauran sun yi aure sun bar ta don akwai wasu lokuta ma da ita kadai ce a gidansu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

"Da iyayena nake zama a baya kuma suna yawan fadin cewa suna fatan ganin ranar da zan yi aure har in haifa musu jikoki."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Xaveline ta sanar da tashar Afrimax ta turanci dake YouTube.

"Ni kaina na so hakan, amma abun takaici sun mutu lokacin da ban yi aure kuma alamu na nuna cewa na yi tsufan da zan samu saurayi. An bar ni ni kadai kuma na yanke hukuncin komawa wurin autarmu."

- Ta kara da cewa.

Wasu daga cikin 'yan uwa, kawaye da makwabta sun bayyana cewa akwai yuwuwar asiri ko maita ce ta hana matar yin aure har ta kai shekarun nan.

Tana rayuwa tare da 'yar uwarta

Bayan mutuwar iyayenta, Xaveline ta koma gidan autarsu mai suna Fatuma Justlene wacce ta damu cewa tsohuwar zata iya fadawa rashin lafiya kuma babu mai kula da ita.

Kara karanta wannan

Bayan Kisan Ummita, Budurwa ta Fallasa Yadda Take Warwarar Kudin Saurayinta Dan Kasar Waje, Tana Neman Shawara

'"Akwai matukar wahala a san dalilin hakan, ta yuwu bata da sa'a ne ko kuma rayuwa bata mata adalci ba."

- Justlene tace.

An rufe babin asiri ko maita saboda na kai ta wurin masu magungunan gargajiya amma hakan bai yi aiki ba saboda har yau babu mashinshini.

Budurwa Tayi wa Banki Fashi Don ta Samu Kudin Maganin Kansar 'Yar Uwarta

A wani labari na daban, wata mata ta yi fashi a bankin Beirut a ranar Laraba da bindigar yara kuma ta fita da dubban daloli domin biyan kudin maganin cutar dake damun 'yar uwarta sakamakon rikicin da ya bakunci Lebanon, Punch ta rahoto.

Wannan dai shi ne na baya-bayan nan a jerin gwano da aka yi a kasar Lebanon, inda aka hana kudaden ajiyar masu ajiya a bankuna kusan shekaru uku, lamarin da ya bar su cikin mawuyacin hali tare da tabarbarewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gwamna Soludo ya Wanke Fulani, Ya Bayyana Wadanda ke Assasa Rashin Tsaro a Anambra

Sali Hafiz ta fitar da wani faifan bidiyo kai tsaye a Facebook na wani hari da ta kai a reshen bankin Blom na Beirut, inda aka ji ta tana kururuwa ga ma’aikatan banki da su saki wasu kudade yayin da aka rufe hanyoyin shiga bankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel