Wani Mutum Ya Nuna Hotunan Layyu Da Guraye Masu Ban Tsoro Da Ya Tono A Gidan Haya Da Ya Shiga A Legas

Wani Mutum Ya Nuna Hotunan Layyu Da Guraye Masu Ban Tsoro Da Ya Tono A Gidan Haya Da Ya Shiga A Legas

  • Wani dan Najeriya mai suna Elkros, ya shawarci mutane su rika yin gyara kafin su shiga gidan haya
  • Matashin ya sha mamaki bayan ma'aikata sun fasa tayil din gidan sun gano layyu da guraye da ake binne
  • Masu amfani da intanet sun yi martani kan labarin inda wasu suma suka rika bayyana abubuwan da suka tarar a gidajen Legas

Twittter - Wani mutum dan Najeriya ya bada labarin abin ban tsoro da ya yi karo da shi bayan ya kama hayan gida a Jihar Legas.

Matashin mai suna Elkros a Twitter ya ce ya biya hayan wani gida amma tayil din bai masa ba.

Juju a Legas
Wani Mutum Ya Nuna Hotunan Layyu Da Guraye Masu Ban Tsoro Da Ya Tono A Gidan Haya Da Ya Shiga A Legas. Hoto: @elkrosmediahub.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ice Prince Zamani, Shahararen Mawakin Najeriya Ya Bayyana Darasin Da Ya Koya Bayan Sako Shi Daga Gidan Yari

Don haka sai ya yanke shawarar fasa tayil din gidan domin a sake masa sabbi. Yayin aikin, ma'aikatan sun gano layyu da guraye da aka binne a karkashin tayil din.

Da ya ke bada labarin a Twitter, Elkros ya ce:

"Na biya hayan gida a Legas a baya-bayan nan, amma tayil din kasan gidan bai min ba, don haka sai na ce zan sake floor din da wasu gyare-gyare. Mai aikin tayil din ya turo min hotunan nan jiya. Ya ce a karkashin tayil din ya gano su.
"Na tambayi manajan gidan sai ya ce wata mace ta zauna a gidan kafin wani na mijin da ya bar gidan. Shawara? Idan za ka iya, ka yi gyara kafin shiga gida. Ka canja floor da POP. Mutanen kasar nan abin tsoro ne. Amma ba matsala idan ba ka yi imani da asiri ba."

Martanin da suka biyo bayan labarin

Basir ya ce:

Kara karanta wannan

Zan So In Ga Mace Ta Zama Shugaban Kasa A Najeriya, In Ji Gwamnan PDP

"Wata kila asirin sa'a ne, kada ka rasa shi, ba komai bane asirin sharri. Akwai wani gida a unguwar mu, duk wanda ya zauna a gidan sai ya siya mota a kalla guda daya kafin ya fita."

Nawti boy ya rubuta:

"Kawai ka shiga sabon gida da aka gina, za ka samu saukin karo da asiri. Amma idan kai mai imani ne, ka sani cewa makaman yakin mu ba na mutum bane."

Obimma Charles ya rubuta:

"Ka san wani abin ban mamaki, zan iya yarda da dan Najeriya da ya ce bai yarda da ubangiji ba, amma ba wanda ya ce bai yarda da asiri ba. Wata kila dai nine."

Forever Dau ya ce:

"Abin sha'awa ne yadda wasu ke ganin asiri ne wasu kuma ke ganin maganin sa'a ne."

Ga sakon da ya wallafa a kasa:

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Kara karanta wannan

Bidiyon Dogarin Sarauniya Elizabeth II Ya Yanke Jiki Ya Fadi Yayin Gadin Akwatin Gawarta

A bangare guda, Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164