Bidiyon Magidanci Yana Shaban Kuka Wiwi, Ya Roki Sassauci Yayin da Aka Yi Gwanjon Motarsa Kan N400,000
- Wani magidanci da ba a ambaci sunansa ba ya sha kuka kamar karamin yaro yayin da gwamnatin Lagas tayi gwanjon motarsa
- An siyar da motar a kan N400,000, farashin da ya karya zuciyar mutumin har ta kai yana rokon sassauci daga gwamnatin
- Hukumar kula da cunkoson ababen hawa ta jihar Lagas ce ta kama motar sannan ta siyar da ita a kan idon mutumin
Lagas - Wani bidiyo mai taba zuciya ya nuno wani dan Najeriya yana sharban kuka wiwi kamar karamin yaro yayin da yake kallo aka yi gwanjon motarsa ga wani a jihar Lagas.
An tattaro cewa jami’an hukumar da ke kula da kame masu take ka’idojin tuki ta jihar Lagas ne suka cafke motar.
A cikin bidiyon, masu sha’awar siyan motar na ta fadin farashinsu sannan mai gwanjon na ta ihun fadin farashin da suka gabatar kan motar mutumin.
Daga karshe dai aka daidaita kuma aka siyar da motar kan N400,000, farashin da ya karya zuciyar mutumin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kafin a siyar da motar, ya sharbi kuka a bainar jama’a sannan ya roki da ayi mai sassauci don motarsa ta dawo hannunsa.
Bidiyon ya karya zukatan mutane a soshiyal midiya.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani a kan gwanjon motar
Kamar yadda ake tsammani, bidiyon ya karya zukatan mutane da dama. Da dama sun je sashin sharhi don caccakar gwamnatin jihar Lagas a kan wannan mataki da ta dauka.
Wasu sun nuna fushinsu yayin da suka ce yin gwanjon ba lallai ya zama maslaha ba. Wasu kuma sun ce gwanda a ci tarar masu laifin sannan a maida masu da motocinsu. Kalli wasu daga cikin martanin a kasa:
@ericamoorebrand ta ce:
“Ku ci su tara sannan ku maidawa mutane motocinsu.”
@eniaiyenfe_ot ya yi martani:
“Wa zai iya nemo mun shi da gaskiya,”
@laviva_bae ya ce:
“Na ji ciwo ganin wannan tsohon yana kuka kan guminsa. Na zata littafi mai karfi ya ce mu zama masu rufa asirin dan uwanmu. Ya Allah ka tayar da wani da zai share hawayen wannan tsohon sannan ka sake dawo da karfin gwiwa a gare shi.
Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas
A wani labarin, Yan Najeriya sun kadu bayan ganin wani bidiyo na wata matashiyar budurwa da ke amfani da jaririn bogi tana bara da rokon kudi a jihar Lagas.
A cikin bidiyon, matashiyar budurwar ta nannade wani abu a tsumman jego sannan tana lallashinsa kamar yaro.
Amma mutumin da take rokon kudin a wajensa shima dan Lagas ne wanda ya san kan abun da suke yi.
Asali: Legit.ng