Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Jana'izarsa Mambobinsu 26 Da Soji Suka Kashe

Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Jana'izarsa Mambobinsu 26 Da Soji Suka Kashe

  • Yan ta'adda masu tada kayar baya sun yi rashin mambobinsu ashirin da 26 sakamakon ruwa wuta
  • Dakarun Sojojin Najeriya a kwanakin nan na samu nasara kan ta'addan da suka addabi al'umma
  • Kwanakin baya Sojojin sun bi yan ta'addan wajen jana'iza suka sake hallaka mahalarta

Kungiyar yan ta'adda ISWAP a ranar Laraba ta gudanar da jana'izar mambobinta 26 da suka mutu a karamar hukumar Gamboru Ngala ta jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar Zagazola Makama, wani masanin harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, rundunar sojin saman Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ne ranar 9 ga Satumba, 2022, rahoton TheCable.

Sojojin sun kai musu farmaki ne a sansaninsu biyu dake Yarwa Kuwa da Sigiri a jihar.

ISWAP
Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Jana'izarsa Mambobinsu 26 Da Soji Suka Kashe
Asali: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa yan ta'addan ISWAP 9 aka kashe a Sigir, yayinda aka kashe 17 a Yarwa Kura.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan Sanda Sun Sheke 'Yan Ta'adda Masu tarin Yawa Bayan Artabu da Ruwan Wuta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar majiyar,

"Jirgin yakin ya yi ruwan wuta kan yan ta'addan dake ganawa a Sigir inda aka kashe mutum 9 da ragargaje wani gini da suka mayar Masallaci da wajen ajiyan kaya."
"A wani harin kuwa da aka kai Yarwa, an kashe yan ta'adda 17 yayinda wasu da dama suka jikkata."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel