An Gwabza Yaki Tsakanin Boko Haram, ‘Yan ta’adda Sun Kashe Kansu da Kansu
- Rigima ta barke a tsakanin ‘yan kungiyar ISWAP da wasu sojojin Abubakar Shekarau a jihar Borno
- Ana zargin ‘Yan Boko Haram sun gamu da fadan da ya fi karfinsu a lokacin da suka je fashi da makami
- An rasa sojojin ‘yan ta’addan ne a lokacin da rundunar sojojin Najeriya ke yi masu lugude da jiragen sama
Borno - Wani mummunan fada ya barke tsakanin mutanen Marigayi Abubakar Shekarau da ‘yan bangaren kungiyar ISWAP da ke ta’adi a Afrika ta yamma.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa rigimar ta kaure ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Satumba 2022, wanda hakan ya jawo aka rasa ‘yan ta’adda da-dama.
Daga cikin wadanda aka kashe a dalilin wannan rigima akwai wani ‘Kundu’, wanda jagoran ‘yan ta’addan ne, haka zalika dai an hallaka wasu sojojin barkatai.
Rikicin ya barke ne a garuruwan Dikwa da Bama, duk a jihar Borno a yankin Arewa maso gabas.
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Kundu da sojojinsa sun je fashi da makami ne sai wasu mayakan kungiyar ISWAP a babura suka yi masu targon rago.
Dakarun na ISWAP sun zo a kan babura shida, kowane babur yana dauke da mayaka uku.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An yi haka - Zagazola Makama
Zagazola Makama wanda masani ne a sha’anin tsaro da rikicin Boko Haram ya tabbatar da aukuwar wannan lamari a shafinsa, yace an kashe mayaka takwas.
A cewar Zagazola Makama, an yi wa ‘yan bangaren Marigayi Shekau illa a harin, yayin da aka samu wadanda suka ji rauni a cikin mayakan kungiyar ISWAP.
Majiyar ta shaida cewa a karshe sojojin Boko Haram sun tsere, sun bar baburan da suke kai. A karshe dai kowane bangare bai ji dadin arangamar da aka yi ba.
"Mummunan yaki ya kaure tsakanin ‘yan ta’addan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayaka da yawa a bangaren ‘yan ta’ddan Boko Haram
Sannan an yi wa wasu sojojin ISWAP rauni. ‘Yan Boko Haram sun arce da kafafunsu, suka bar baburansu a hannun ‘yan kungiyar ISWAP."
- Zagazola Makama
Garkuwa da mutane
Yayin da ake fama da yawaitar satar mutane, kun ji labari cewa Jami’an ‘yan sanda sun tashi tsaye domin kawo tsaro da zaman lafiya a Najeriya.
A makon nan aka ji labari Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Edo su hallaka ‘yan bindiga a Uhunmwondem sun ceto wani jariri da aka dauke shi.
Asali: Legit.ng