Jonathan Ya Yi Wata Ganawar Sirri da IBB, Abubakar a Birnin Minna, Jihar Neja

Jonathan Ya Yi Wata Ganawar Sirri da IBB, Abubakar a Birnin Minna, Jihar Neja

  • Tsoffin shugabannin uku, Goodluck Jonathan, Badamasi Babangida da Abdulsalami sun gana a jihar Neja
  • A ganawar ta yau Alhamis 15 ga watan Satumba, Jonathan ya ce ya kai ziyara ce kawai irin ta yau da kullum
  • Jonathan ya ce ya je gaisuwar rashin lafiya ne ga Janar Abdulsalami bayan dawowarsa daga kasar waje jinya

Minna, jihar Neja - Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya kai wata ziyarar kai da kai ga tsoffin shugabannin soja; Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar a birnin Minna ta jihar Neja

Tsohon shugaban ya gana da tsoffin shugabannin na soji ne a gidajensu da yammacin yau Alhamis 15 ga watan Satumba, Vanguard ta ruwaito.

Goodluck Jonathan ya gana da IBB da Abdulsalami
Jonathan Ya Yi Wata Ganawar Sirri da IBB, Abubakar a Birnin Minna, Jihar Neja | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake amsa tambayoyi daga 'yan jarida, Goodluck ya ce ya kawo ziyarar ne kamar yadda ya saba ga tsoffin shugabannin.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Baiwa Yan Wasan Gudu Kyautar N200m Da Lambar Yabo

A kamalansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ziyara ce ta yau da kullum kawai musamman kasancewa ta mafi kankanta a cikin tsoffin shugabannin.
"Haka kuma dama ce a gareni don na ziyarci Janar Abdulsalami ABubakar da ya dawo daga jinya a kasar waje sannan na ziyarci Janar Babangida."

Bayan Shafe Watanni Yana Jinya A Waje: Tsohon Shugaban Najeriya Ya Dawo Kasar

Janar Abdulsalami Abubakar ya shafe lokaci a kasar waje, inda ya zauna a can domin jinyar rashin lafiya da ya yi.

Rahoto ya ce ya dawo gida Najeriya a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta.

Ya iso kasar ne a cikin jirgin shugaban kasa wacce ta sauka a filin jirgin sama na Minna da misalin karfe 3:30 na yamma, jaridar Thisday ta rahoto.

Matarsa, Justis Fati Lami Abubakar na cikin tawagar Janar Abubakar kuma sun samu tarba daga manyan yan Najeriya kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Mance Da Batun Tinubu, Ya Fadi Wanda Zai Sa Ya Gaji Buhari Da Yana Da Iko

A wani labarin na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce akwai wadanda su ya kamata su ke tallata nasarorin da gwamnatinsa ta samu, amma sam ba sa yin hakan, TheCable ta ruwaito.

Buhari ya bayyana haka ne a yau Talata 13 ga watan Satumba a wata ziyarar bude ayyuka da ya kai jihar Imo ta kudancin Najeriya.

Shugaban ya ce, idan aka yi duba cikin tsanaki da irin albarkatun kasa da gwamnatinsa ta samu, za a fahimci irin kokarin da ya yi a mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.