Sokoto: Yan Bindiga Sun Kai Hari Wani Gari Sun Sace Kayan Abinci
- Mutanen garin Gwandi a Jihar Sokoto sun koka kan yadda yan bindiga suka mamaye garinsu suna sace musu kayan abinci
- Mazauna garin sun ce wasu daga cikinsu sun yi yunkurin komawa gidajensu don su kwaso kayan abinci amma suka tarar yan bindiga sun mamaye garin
- Bayan komawa sansanin yan gudun hijiran, sun yi kira ga gwamnatin jiha da tarayya su taimake su da magunguna da abinci sannan a tura jami'an tsaro su fatattaki yan bindigan
Sokoto - Mazauna garin Gwandi mafi yawancinsu maza sun yi yunkurin komawa gidajensu su kwaso kayan abinci da wasu abubuwa don iyalansu da ke tsugune a makarantun frimari a hedkwatar karamar hukumarsu amma yan bindiga da suka mamaye garin suka hana su.
Wasu daga cikin mazauna garin sun shaida wa TVC News a sansanin yan gudun hijira na wucin gadi a Kebbe cewa yan bindigan sun kutsa gidajensu sun sace musu kayan abinci.
Mun Gaji Da Kashe Mana Mazaje Da Makiyaya Ke Yi: Mata Sun Yi Zanga-Zanga A Jihar Arewa, Sun Tare Titi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun ce wasu daga cikin mutanen da suka koma kauyen sun sha da kyar kuma wadanda suka tafi kan babura sun tsere sun bar wa yan bindigan baburan sun dawo Kebbe.
Yan gudun hijira sun yi kira da gwamnati ta taimaka musu da kayan abinci da magunguna
Mutanen garin da wasu wadanda suka rasa muhallinsu daga wasu wurare suna kira ga gwamnarin jiha da tarayya ta taimaka musu da abinci su kara kan abinda karamar hukuma ke basu.
Sun kuma yi kira da cewa a tura jami'an tsaro zuwa garuruwansu domin su fatattaki yan bindigan daga garuruwansu.
A taimaka mana da magunguna - yan gudun hijira
A cewarsa, ba za su iya komawa gonakinsu ba idan yan bindigan suka cigaba da zama a garin kuma hakan zai kara jefa su cikin mawuyancin hali.
Sun kuma roki gwamnati ta taimaka musu da magunguna da gadaje, inda suka ce damina ya sa sauro sun yada wa yara da matansa zazabin cizon sauro.
Wani mazaunin garin ya ce yan bindigan sun yadda zango a garinsu kuma suna amfani da gidajensu don ajiye wadanda suka yi garkuwa da su.
'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu
A wani rahoton, Mustapha Imam, daya daga cikin mutanen da yan bindiga suka sace jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja ya ce ya yi wa yan bindiga magani a lokacin da ya ke tsare a hannunsu.
A wani bidiyon da Tukur Mamu, mawallafin Desert Herald wanda ya taimaka wurin tattaunawa don ganin an sake su, fasinjan ya bayyana zamansa a hannun yan bindigan a matsayin 'lamari matukar muni'.
Asali: Legit.ng