Sanatoci Za Su Kashe Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati 400 a shekarar 2023
- ‘Yan Majalisar Dattawa sun yi zama da wasu shugabannin ma’aikatun gwamnatin tarayya a Najeriya
- Kwamitin kudi na majalisar ya yi tir da yadda wasu MDAs suke cin kudi ba tare da sun tatso komai ba
- Shugaban kwamitin, Olamilekan Adeola yayi gargadi da cewa za a rusa hukumar da ba ta kawo kudi
Abuja - Shugaban kwamitin tattalin arziki a majalisar dattawa, Sanata Olamilekan Adeola yace akwai maganar soke mafi yawan ma’aikatun gwamnati.
Vanguard ta rahoto Olamilekan Adeola a ranar Laraba, 14 ga watan Satumba 2022 yana cewa za a kashe fiye da 400 daga cikin ma’aikatu 541 da ake da su.
Sanata Olamilekan Adeola yake cewa za a iya yin wannan aiki ne a shekarar badi kamar yadda kwamitin Stephen Orosanyeya ya ba gwamnati shawara.
A lokacin da Stephen Orosanyeya da kwamitin shi suka yi wannan aiki, sun yi la’akari da samun kudin-shiga, suka ce ma’aikatu 106 kacal ya kamata a bari.
Shugabannin MDAs sun je majalisa
Punch tace ‘Dan majalisar ya yi wannan bayani jiya a taron da suka yi da shugabannin MDAs kan yadda za a samu kudin aiwatar da kasafin kudin badi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Adeola ya zauna da Dr. Rufus Ebegba wanda shi ne shugaban hukumar tarayya ta NBMA, ya yi korafi a kan karancin kudin da ake samu daga ma’aikatarsa.
Da yake bayani Dr. Rufus Ebegba yace N2.5m kadai NBMA ta iya samu a shekarar nan, akasin N5m da aka saba duka shekara, amma an ware masu biliyoyi.
Sanatan mai wakiltar yammacin Legas a majalisar dattawa ya fusata da jawabin wannan DG, da ya ji sun batar da karin N500m, amma ba su iya tatso N5m ba.
Kamar yadda Adeola ya fadawa shugaban na NBMA, lokacin rashin tatsar kudi ya wuce domin duk wata hukumar da ba ta kawo kudin-shiga, za a iya shafe ta.
Sanata Olamilekan Adeola ya ja-kunne
“Babu abin da zai sa a fasa dabbaka aikin kwamitin Stephen Orosanye saboda halin tattalin arzikin da muka samu kasar nan ciki a wannan yanayi.
Gwamnati tana bukatar kudin shiga domin ta aiwatar da kasafin kudi, ba za cigaba da bada kudi ga hukumomin da ba su kawo kudin shiga ba.”
Yajin-aiki a Jami'o'i
Kuna da labari gwamnatin Muhammadu Buhari na neman tursasawa malaman jami’a su koma aiki, an shigar da karar kungiyar ASUU a kotun NIC
An kuma ji ‘Yan kungiyar ASUU a Najeriya sun yi tanadin gawurtattun Lauyoyi kusan 50 da za su kare su, ba tare da an biya su sisin kobo a kotu ba.
Asali: Legit.ng