Gwajin DNA: Bayan Shekaru 20 Da Aure, Magidanci Ya Gano Dukkan 'Yaya 5 Ba Nasa Bane

Gwajin DNA: Bayan Shekaru 20 Da Aure, Magidanci Ya Gano Dukkan 'Yaya 5 Ba Nasa Bane

  • Wani mutumi ya gano dukkan yayan da matarsa ta haifa tsawon shekaru 20 da suke tare ba nasa bane
  • Mutumin dan shekaru 57 ya gano hakan ne bayan gwajin DNA da ya yiwa dukkan yaran biyar
  • Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan lamarin mai ban mamaki da takaici

Da yiwuwan auren shekaru 20 ya mutu bayan maigida ya gano dukkan 'yaya biyar da matarsa ta haifa ba nasa bane.

Mutumin ya gudanar da binciken asibiti na gwajin DNA kan dukkanin yaran.

Henry Nwazuruahu Shield, tsohon hadimin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bada wannan labari a shafinsa ba Facebook.

Yace shekarun mutumin 57 yanzu.

DNAGU
Gwajin DNA: Bayan Shekaru 20 Da Aure, Magidanci Ya Gano Dukkan 'Yaya 5 Ba Nasa Bane
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

A cewa Henry, yanzu ana ba mutumin hakuri.

Henry yace:

"Wani mutumi dan shekaru 57 ya gudanar da gwajin DNA kan dukkan yayansa 5 kuma ya gano dukkansu ba 'yayansa na gaske bane. Shekaransa 20 da aure. Ana ba shi hakuri yanzu."

Martanin jama'a

Isah Kani Tsangarwa yace:

"Subahanallahi, to Allah ya kiyaye, to shi me ya kaishi gwajin,? Ko taurin Kai yaga suna Masa?
To koma dai mene mugunji mugun gani Allah kayi Mana maganinsa alfarmar sayyadina rasulillahi S.A.W."

Musa Ashiru Yawale:

"Irin haka ne da yawa zaka ji ance wani ya kashe ubanshi ko ya bugi uban shi, dan haka mutane ku lura da shigi da ficen matan ku."

Malhama Joda Muhammad Usman:

Wani shari'an sai a lahira

Muzzammil Lawal Gulmah yace:

"Dama allah ya ce ولا تجسسوا
Amma shi sai da ya tsallake iyaka
Yanxu ya ja wa kansa bakin ciki da kunci a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Buɗe Wa Jami'an 'Yan Sanda Wuta, Rayuka Sun Salwanta

Allah ubangiji ya sauwaka ya tsare mana mutuncinmu"

Maryama Muhammad Saniey

Kai amma wannan Mata Allah yayi karya wlh, haba itakuwa wannan cin amana da meyayi kama, to Allah ya kyauta

Peter Lamindi

Bayan shekaru 20 na aure kuma har da yaya 5 kuma shima shekarunsa 57. A Gaskiya banga anfanin wannan gwaji DNA ba domin kuwa rayuwan da Da yake lallabawa sai dai ta tarwatse yanzu saboda wani DNA, gwara a hakura da wani bincike don ba zai taimaka ba sai dai ya kawo high BP. Duk wani buncike za'ayi a lahira. Nawa ra'ayin

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel