Mata Da Kudi: Yadda Yan Mata Suka Mato Kan Matashi Dan Tsurut Da Ke Tuka Dankareriyar Jeep Cikin Salo A Bidiyo

Mata Da Kudi: Yadda Yan Mata Suka Mato Kan Matashi Dan Tsurut Da Ke Tuka Dankareriyar Jeep Cikin Salo A Bidiyo

  • Wani hadadden matashi mai suna Katuosis Babayao wanda ke da karamin jiki ya nuna yadda yake iya tuka tsadaddiyar motarsa
  • Ya aikata hakan ne bayan masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun fara al’ajabi kan yadda yake iya tuka motar
  • Bayan ya saki bidiyon, wasu yan mata sun cika sashinsa na sharhi da zantuka, sun tambaya ko za su iya zama masoyansa

Jama’a sun yi cece-kuce bayan bayyanar bidiyon wani mutum dan yana nuna yadda yake iya tuka tsadaddiyar babbar motarsa duk da kasancewarsa dan tsurut.

Mutumin mai suna Katuosis Babayao ya yada bidiyon don cire kokwanto a zukatan mutanen da ke tunanin ba zai iya tuki ba ko kuma wadanda ke mamakin ya yake tuka motar.

Matashi
Zan Zama Bebinka: Yan Mata Sun Mato Kan Matashi Dan Tsurut Da Ke Tuka Dankareriyar Jeep Cikin Salo A Bidiyo Hoto: TikTok/@katuosis
Asali: UGC

A cikin bidiyon, Babayao ya nuna yadda aka kera masa kujerarsa na zaman tuki zuwa na musamman. Kujerar ta fi ainahin kujerun motoci da aka saba gani tsawo domin bashi damar ganin hanya da kyau.

Kara karanta wannan

Ina Mai Rokonka Dan Allah, Ka Kula Da Diyata: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Ya Roki Surukinsa A Bidiyo

Hakazalika, an kera masa wajen sa kafa ya fi wanda aka saba gani tsawo don ya samu kafafuwansa su dunga kaiwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bangare na bidiyon, ya dare kan kujerar direba sannan ya ja motar wanda hakan ya birge mabiyansa a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Mabiya TikTok sun yi martani

A halin da ake ciki, mabiya shafinsa na TikTok sun yi martani a kan bidiyon da ya wallafa. Wasu daga cikin yan matan sun ce suna so su zama bebinsa. Sauran sun jinjina masa kan yadda ya tsara motarsa daidai da yanayinsa.

@Shelly Wangui ta ce:

“Bebinka guda daya tal kuma ni ce.”

@wa T ta yi martani:

“Nima ina so na zama bebinka.”

@VillageBoy@CityDream ya ce:

“Ina kaunar mutumin da kake.”

@Steve Wa Beatoh ya ce:

“Baka fahimcemu bane dan uwa, muna bukatar ganin yadda kake tuka bebinka ta 1 ne.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Mutumin da Ya Shiga Jirgin Sama, Ya Bai wa Kowanne Fasinja N42k Ya Dauka Hankali

  • Ni Ba Yarinya Bace: Wata Budurwa 'Yar Tsurut Ta Fashe Da Kuka Bisa Yadda Wasu Ke Mata Kallon Yarinya

A wani labarin, wata matashiya mai karamin jiki da ke nishadantar da mutane a dandalin TikTok ta bayyana cewa ita din ba karamar yarinya bace domin ta balaga.

Matashiyar mai suna @itzamealiaa a TikTok tana da karamin jiki da kuma siriryar murna irin ta kananan yara kuma hakan yasa mutane da dama yanke hukuncin cewa ita din yarinya ce kankanuwa.

A wani bidiyo da ta yada a dandalin, budurwar wacce ke cike da karfin gwiwa ta bayyana cewa tana fama da wani nau’in cuta ne da ke kankantar da mutun wanda shine dalilin kasancewarta yar tsurut..

Asali: Legit.ng

Online view pixel