“N758,000 Nake Samu Duk Wata”: Matashi Dan Najeriya Da Ke Zaune A UK Ya bayyana Albashinsa Da Sauran Abubuwa
- Wani dan Najeriya mai digirin digirgir ke zaune a UK ya yi karin haske kan yadda rayuwar Turai take
- A cewar mutumin mai suna Jaja, albashinsa duk wata ya kai kimanin N758,000, amma yana kashe kimanin N636,000 kan abubuwan bukata
- Wannan bayani nashi ya haddasa cece-kuce a tsakanin yan Najeriya a Twitter, wasu sun caccakesa kan korafin da yayi
UK – Wani dan Najeriya da ke zaune a UK ya ce mutanen da ke barin kasar a yanzu haka za su gamu da tsadar rayuwa da ke faruwa a chan.
A cewar mutumin mai suna Jaja, mutanen da ke zaune a UK yanzu haka suna fama ne da tsadar rayuwa.
Jaja wanda ya mallaki digirin digirgir, ya sha cacca daga wajen wani mai amfani da Twitter @_Nache_1, wanda ya zarge shi da yawan korafi ba tare da ya bayyana yawan kudin da yake samu ba.
@_Nache_1 ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ku mutanen nan sai kuyi ta korafi game da tsadar rayuwa a UK amma ba za ku bari mu san nawa ake biya ba a aikin da kuke yi da kuma nawa kuke kashewa."
Nawa nake samu da kuma nawa nake kashewa kan abubuwan bukata a UK
Jaja ya yi martani ta hanyar bayyana albashinsa duk wata da kuma nawa yake kashewa kan abubuwan bukata. Ya ce:
“Wadanda ke shirin fecewa daga Najeriya zuwa UK a wannan lokaci za su fada kai tsaye cikin tsadar rayuwa.
“Wadanda ke zaune a nan da wadanda suka samu matsuguni suna fama sosai. Allah ya albarkacemu mu dukka.
“Albashina yanzu duk wata ya kai £1550 bayan an cire kudade. Abun da nake kashewa duk wata £1300 banda na ajiya. Ina fatan wannan zai taimaka.”
Kalli wallafar a kasa:
UK na daya daga cikin kasashen da yan Najeriya ke son zuwa a Turai.
Jama’a sun yi martani
@davidfatunmbi ta ce:
“Daya daga cikin tsoffin kawayena wacce ke da gida a Landan ta baro UK zuwa Lagas a farkon shekarar nan saboda, a cewarta, tsadar rayuwa na kara tabarbarewa a UK kuma cewa zai fi mata sauki a Najeriya. Kamar dai ta hango gaba.”
@otega_el ya kara da cewa:
“Ya kamata yan Najeriya su gane cewa wasu lokutan irin wadannan wallafar ba wai don a sace maku gwiwa bane. Ku zo idan kuna son zuwa. Duk da halin da UK ke ciki ya fi 9ja ta fuskacin zamantakewar rayuwa. Amma kada ku bari wani ya baku tsatsuniya game da kasar.”
Zaman Dubai Sai An Shirya: Bidiyon Wasu Karatan Maza Suna Aikin Wanke-Wanke Don Samun Na Kashewa
A wani labarin, wani dan gajeren bidiyo da aka wallafa a TikTok ya nuna cewa mutane da dama da ke zuwa kasar waje don aiki suna shan fama don tara kudade, suna yin harda da irin ayyukan da ba za su iya yi ba a kasarsu.
A cikin bidiyon, an gano karatan maza a wani wuri da yayi kama da wajen siyar da abinci suna wanke tulin kwanuka. Sun mayar da hankali sosai wajen ayyukansu yayin da suke sanye da kayan girki.
Wasun sun suna ta dan hira yayin da suke aikatau. Gaba daya kewaye suke da kwanuka masu datti wadanda ke jiran wanki.
Asali: Legit.ng