An Datsi Tashar Yanar Gizon INEC Daga Asiya a Lokutan Zaben Gwamnan Jihar Ekiti da Osun
- Rahoto daga INEC ya ce, wasu madatsa sun yi kokarin farmakar tashar yanan gizon hukumar a zabukan Ekiti da Osun
- Ana shirin zaben 2023, hukumar INEC ta bayyana wata maganar da ka iya jawo rashin natsuwa ga 'yan Najeriya
- Hukumar ta INEC ta bayyana yadda lamarin ya faru, kuma ta bayyana irin matakin da take dauka a kai
FCT, Abuja - Akwai yiwuwar a samu matsala a babban zaben 2023 yayin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da sabon tsaiko a shafinta na duba sakamakon zaben (IReV).
Wani tahoton TheCable ya ce, INEC ta bude sirri, tace wasu madatsa daga nahiyar Asiya sun datsi tashar duba sakamakon zabe a zabukan da suka kammala na jihohin Ekiti da Osun.
Shugaban INEC, Mahmud Yakubu ne ya bayyana wannan lamari a yau Juma'a 9 ga watan Satumba a Abuja yayin da yake magana a wani taron da ya shafi jami'an sakamakon zabe.
Kungiyar farar hula ta YIAGA Africa ce ta shirya taron domin kaddamar da ajandar rahoton tattara sakamakon zabe na ERAD.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yakubu ya ce, tashar yanar gizon ta samu hare-hare daban-daban daga madatsa da watakila ke son jirkita sakamakon zabe, rahoton NewsWire.
A cewarsa:
"Wani abin damuwa na fasaha shine ganin maimaituwar yunkurin datsar tsarin tsaro don farmakar tashar ta yanar gizo."
“ Injiniyoyin mu sun kai rahoton wani farmakin madatsa a tasharmu a yayin zabukan gwamnan Ekiti da Osun, wasu daga cikin farmakin sun fito ne daga yankin Asiya. Na yi farin cikin sanar daku cewa basu yi nasara ba."
Ya ce, hukumar na kara mai da hankali ga tsaron tashar ta yanar gizo, duk da haka dole ne hukumar ta sake sanya ido domin tabbatar da an tsare sakamakon zabe.
INEC Ta Sanar Da Ranar Wallafa Ta Karshe Na Sunayen Dukkan Yan Takara A Zaben 2023
A wani labarin, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, za ta saki sunayen dukkan yan takaran da zasu yi musharaka a zaben kasa na shekarar 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja inda ya halarci taron kungiyar Centre for Democracy and Development (CDD).
A cewarsa, hukumar zata saki sunayen yan takaran shugaban kasa, Sanatoci da yan majalisar wakilai ranar 20 ga Satumba, 2022, rahoton Channels.
Asali: Legit.ng