Yajin aikin ASUU: Jonathan Ya Jefa Mu Halin da Ake Ciki a Yau Inji Ministan ilmi
- Ministan ilmi na kasa, Adamu Adamu ya yi bayanin inda aka kwana a kan batun yajin-aikin malaman jami’o’i
- Malam Adamu Adamu yana ganin Goodluck Jonathan tayi wa ASUU alkawarin da ya fi karfin gwamnati a 2013
- Ministan yace da zarar kungiyar ASUU ta amince da tayin da ya yi masu, za a biya su kudinsu a take-yanke
Abuja - A wata hira ta musamman da aka yi da Ministan ilmi na kasa, Adamu Adamu, ya yi bayani kan rikicin gwamnatin tarayya da ‘Yan ASUU.
Malam Adamu Adamu ya yi wa tashar Channel’s TV bayani game da tayin da gwamnatin Muhammadu Buhari tayi wa malaman jami’o’in kasar.
Da aka tambayi Ministan a kan silar rigimar gwamnati da kungiyar ASUU na shiga yarjejeniyar 2013 a lokacin da babu kudi, ya yarda da wannan batu.
Adamu Adamu ya yarda cewa gwamnatin Goodluck Jonathan ta sa hannu cewa za ta fitar da N1.3tr a shekaru shida, alhali babu kudin da za ayi hakan.
“Tare da ganin girman gwamnatin Goodluck Jonathan, ba na tunani lokacin da ta sa hannu a wannan yarjejeniya, tayi nufin cika alkawari, domin babu kudin nan.”
- Malam Adamu Adamu
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mun sha bam-bam da Jonathan
Sai dai wannan karo, Ministan ya shaidawa ‘dan jaridae cewa idan har malaman jami’a suka karbi tayin gwamnati, an kawo karshen matsalar ASUU.
An ji Adamu Adamu yana cewa Muhammadu Buhari na kokarin magance duk wani rikici da malaman jami’a kafin wata gwamnati ta karbi mulki a badi.
Ministan yake cewa wannan karo gwamnatin tarayya ta gabatarwa ma’aikatan jami’o’i tayin da za a iya cika su nan-take, a maimakon dogon alkawari.
"Wannan karo mun kawo masu tayin da tashi daya ne kurum. Da zarar sun amince da yarjejeniyar, abu ne wanda za a iya fara biyansu nan ta ke.
Ba kamar Jonathan da ya yi alkawarin zai biya Naira Tiriliyan 1.3 a cikin shekaru shida ba."
- Malam Adamu Adamu
Kamar yadda bidiyon tattaunawar ya nuna, duk da kalubalen da ake fuskanta na bashi da za a ci a 2023, Adamu yace ba za su bari ASUU ta kai su bango ba.
An hana Malamai albashi
Kwanakin baya Adamu Adamu ya shaida cewa gwamnatin tarayya ba za ta biya malamai albashin tsawon lokacin da suka shafe su na yajin-aiki ba.
Daga baya an ji labari shugaban kungiyar ASUU na kasa baki daya ya maida martani ga kalaman da Ministan ilmi ya yi, yace babu dalilin hana su kudinsu.
Asali: Legit.ng