Alkali Ya Tura Dan Sufetan Yan Sanda Gidan Yari Kan Satar Motar N52m A Legas
- Kotun majistare da ke zamanta a Yaba Legas ta bada umurnin a kai wani Damilola Areje gidan yarin Kirikiri har sai ya cika ka'idan beli
- Areje, wanda mahaifinsa dan sanda ne mai mukamin sufeta ya tsinci kansa a gidan yarin ne bayan gurfanar da shi kan satar mota da kudi
- Wata mata, Miss Chiemelu ta yi kararsa kan cewa ya sace mata mota kirar Marsandi wanda kudinta ya kai Naira miliyan 52 kuma ya sace mata Bitcoin na $700
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Legas - Alkalin kotun majistare da ke zamanta a Yaba a Legas ya bada umurnin a tsare wani Damilola Areje, a gidan yari kan satar mota, har sai ya cika ka'idojin beli.
Damilola, wanda iyayensa yan sanda ne, an bada belinsa kan kudi Naira miliyan 3 da mutane biyu wadanda ke da takardan biyan haraji na akalla shekara biyu da kuma a kalla gida daya a unguwan da kotun ke da iko.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
The Punch ta rahoto cewa Damilola a watan Yuli, ya tsere da mota kirar Marsandi 2019 GLE 43, da kudinta ya kai Naira miliyan 52, da kudin zamani na Bitcoin da darajarsa ya kai $700 malakar wata yar kasuwa, Nneka Chiemelu.
A cewar Miss Chiemelu, Damilola, wanda mahaifinsa Sufeta Adegbola Areje dan sanda ne, ya sace motarta daga gidanta da ke Lekki Phase 1 ya kuma tsere da Bitcoin da darajarsa ta kai $700 da daya cikin abokan cinikayarta ya biya a asusunsa a ranar Juma'a 22 ga watan Yulin 2022 misalin karfe 4.05 na yamma.
Bayan kimanin wata biyu yan sanda na bincike, an gurfanar da Damilola a kotu kan zargin sata, kuma an tsare shi a gidan yari na Kirikiri har sai ya cika ka'idar belinsa.
The Punch ta tattaro cewa har yanzu Chiemelu ba ta karbo motarta daga hannun yan sanda ba, don an bukaci ta rubuta bukatar karbar motar a hukumance.
Lauyanta, Michael Eyinnaya, ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng Hausa cewa za su mika bukatar karbar motar daga hannun yan sanda.
Martanin kakakin yan sandan Legas Benjamin Hundeyin
Da aka tuntube shi domin samun karin bayani kan lamarin, a yammacin ranar Talata, mai magana da yawun yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce zai yi bincike kan batun.
Ya ce:
"Ina can ina fama da wasu ayyukan. Ban samu labarin ba, amma zan yi bincike sannan zan sanar da kai duk abin da na gano."
An kama sojan gona da kayan hukumar FRSC dauke da katin shaidar aikin soja a Kano
A bangare guda, Hukumar FRSC da hukumar yan sanda sun kama wani mutum mai suna Injiya Gude Ude a jihar Kano da kayan jami'an hukumar kiyaye hadura FRSC kuma dauke da katin shaidar aikin sojan a garin Kano.
Sanarwan da hukumar FRSC ta bayar mai dauke ta sa hannun mukadashin Secta Kwamanda, Ahmed T. Mohammed ta cean kama Ude ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2018 a titin Kaduna - Kano a yayin da rundunar ke gudanar da wata kewaye na musamman da akayi wa take da "Operation Zero"
Asali: Legit.ng