Hoto: Mahaifiya Ta Yi Dambe Da Damisa Da Ya Yi Yunkurin Halaka Danta A Indiya

Hoto: Mahaifiya Ta Yi Dambe Da Damisa Da Ya Yi Yunkurin Halaka Danta A Indiya

  • Wata baiwan Allah a kasar Indiya ta nuna jarumta a yayin da wani damisa ya taho yana son halaka danta mai rarafe
  • Rahotanni sun nuna cewa matar ta fita waje cikin dare ne domin danta ya yi fitsari kwatsam sai daminsan ya afka musu da hari yana son fizge yaron
  • Matar ta ki sake wa daminsa danta suka rika kokawa har sai da mutanen gari suka ji ihunta suka fito kawo mata dauki sannan damisan ya tsere cikin daji

Indiya - Wata mahaifiya ta yi kokawa da daminsa da hannunta domin ceto danta mai rarafe daga bakin damisa, kamar yadda jami'ai suka sanar ranar Laraba, rahoton Channels TV.

Archana Choudhary ta fita daga gidanta da ke Madhya Pradesh a daren ranar Lahadi saboda yaronta dan shekara daya da wata uku yana son yin fitsari.

Kara karanta wannan

Hotunan Ummi, Kyakkyawar Budurwar Da Ta Rasa Ranta A Farmakin Da Yan Bindiga Suka Kai Bankunan Kogi

Mahaifiya
Mahaifiya Ta Yi Kokawa Da Damisa Don Ceto Danta A Indiya. Hoto: @channelstv.
Asali: Twitter

Yadda daminsan ya kai wa matar da danta hari

Wani damisa da ake kyautata zaton ya tsere ne daga gandun daji na Bandhavgarh ya afka musu, jami'i Sanjeev Shrivastava ya shaidawa AFP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kai musu hari ya yi kokarin cizon kan yaron amma mahaifiyar ta tunkare shi don ceto danta, in ji shi.

Damisan ya cigaba da kokarin kwace yaron har sai da mazauna kauyen suka ji ihunta suka kawo mata dauki.

Daga nan ne damisan ya tsere ya shiga daji.

Shrivastava ya ce:

"An kwantar da ita a asibiti. Yanzu ta fara samun sauki. Jinjirin shima yanzu yana samun sauki."

Mahaifiyar ta samu rauni a kirji da cikinta yayin da shi kuma danta akwai raunin cizo a kansa.

Jaridar Times of India ta ce an fara neman daminsan da nufin mayar da shi gandun dajin an kuma bukaci mazauna kauyen su dena fitowa waje cikin dare.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Damke Tukur Mamu, mai sulhu tsakanin yan bindiga da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna A Kasar Misra

Ana samun karuwar rikici tsakanin dabobin daji da mutane a nahiyar South Asia a yayin da aka fadada birane dazuka kuma suna tsukewa.

Alkalluman gwamnatin Indiya game da adadin damisa da ke duniya

Kimanin mutum 225 ne suka mutu sakamakon harin daminsa tsakanin 2014 zuwa 2019 a India a cewar alkalluman gwamnati.

Fiye da daminsa 200 ne masu farauta suka kashe ko kuma lantarki tsakanin 2012 da 2018, alkalluman suka nuna.

Kimanin kashi 70 cikin 100 na daminsan da ke duniya suna kasar indiya ne kuma an kiyasta yawansu ya kai 2,967 a 2018.

Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

A bangare guda, bidiyon wani matashi dan Najeriya yana tsokanar mahaifiyarsa cikin raha saboda yanayin shigarta ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

A bidiyon da aka daura a TikTok, matar na shirin gida gida sai dan nata ya hana ta, sannan ya umurci mahaifiyar tasa da ta koma daga inda ta fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164