Jinjiri Dan Wata 7 Da Mata 4 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Jigawa

Jinjiri Dan Wata 7 Da Mata 4 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Jigawa

  • Mutane hudu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a karamar hukumar Guri, Jigawa
  • Kakakin rundunar yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu ya bada sunan wadanda suka rasun; mata hudu da jinjiri dan wata bakwai
  • Shiisu ya ce rahotanni sun nuna kwale-kwalen ta kife ne amma direban ne kadai ya tsira da rai kuma an fara bincike

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Jigawa - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Jigawa ta tabbatar da rasuwar jinjiri dan wata bakwai da mata hudu a hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guri.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu, ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a Dutse, ranar Laraba, rahoton Daily Trust.

Hatsarin Kwale-kwale
Hatsarin Kwale-Kwale Ya Kashe Mata 4 Da JinJiri Dan Wata 7 A Jigawa. Hoto: @daily_trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama wata malamar coci dake sayen yara kanana kan kudi N50,000

Yadda hatsarin kwale-kwalen ya faru - Shiisu

Shiisu ya ce:

"A ranar Talata, misalin karfe 6, bayanai da muka samu ya nuna a ranar misalin karfe 4.30 na yamma mata hudu da jinjiri dan wata hudu sun hau kwale-kwale daga Nuguru Jihar Yobe zuwa Kauyen Adiyani a karamar hukumar Guri, Jihar Jigawa.
"Amma, kwale-kwalen ya kife dab da kai wa inda za su tafi. Direban ya tsira da ransa, yayin da fasinjojin suka nutse."

Ya ce mutanen yankin sun yi kokari ceto fasinjojin, ya kara da cewa sun ciro gawarwakin su.

Kakakin yan sandan ya ce an kai gawarwakin cibiyar lafiya ta Adiyani inda likita ya tabbatar sun rasu.

Sunayen wadanda suka rasu a hadarin kwale-kwalen Jigawa - Shiisu

Shiiusu ya bada sunayen wadanda suka rasu kamar haka Oneyaniwura Kasagama, 50; Lafiya Bulama, 40; Badejaka Kasagama, 40; Gimto Kasagama, 40 da Mai Madu Bulama, jinjiri dan wata bakwai.

Kakakin yan sandan ya ce dukkan wadanda suka rasu mazauna kauyen Adiyani ne, ya kara da cewa an fara bincike kan afkuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama

Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara

A wani rahoton, al'umman garin Ogbinbiri da ke karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa sun shiga alhini a jajiberin sabuwar shekara sakamakon mutuwar wani fasto da wasu mutane shida.

A cewar idon shaida, lamarin ya afku ne lokacin da wasu kwale-kwale biyu suka yi karo, inda suka kife a ranar Laraba, 31 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164