Gwamna Bagudu Na Jihar Kebbi Ya Kori Kwamishinoninsa Saboda Wasu Dalilai

Gwamna Bagudu Na Jihar Kebbi Ya Kori Kwamishinoninsa Saboda Wasu Dalilai

  • Gwamnan jihar Kebbi ya sanar da korar dukkan kwamishinoninsa, inda ya rusa majalisar zartarwarsa
  • Gwamnan ya kuma mika godiya garesu, inda ya bayyana nan ba da jimawa zai nada sabbin da za su maye gurbinsu
  • An sha samun lokuta daban-daban da gwamnoni ke korar mambobin majalisar zartarwarsu saboda wasu dalibai daga gwamnati

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kebbi - A yau Laraba 7 ga watan Satumba ne gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya ruguza majalisar zartarwa ta jiharsa, inda ya sallami dukkan kwamishinoninsa.

Premium Times ta ruwaito cewa, gwamnan ya ce rusa majalisar zartarwar tasa ta fara aiki ne nan take daga ranar ta Laraba.

Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohin Arewa dake fama da matsalar tsaro a shekarun baya-bayan nan.

Gwamna Bagudu na Kebbi ya kori dukkan kwamishononinsa
Gwamnan jihar Kebbi ya kori kwamishinoninsa, ya fadi dalilai | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Batun nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Babale Yauri, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kungiyar Kwallon Chelsea Ta Sallami Kocinta, Thomas Tuchel

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga dukkan kwamishinonin nasa da suka yi aiki tukuru.

Sanarwar ta ce:

“Gwamna ya nuna matukar godiya da irin gudumawar da kowane daga cikin kwamishinoninsa ya ba da tare da gode musu bisa ba da lokaci da suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya da ci gaban jihar a lokacin da suke rike da mukamansu.

A bangare guda, ya bayyana cewa, nan ba da jimawa zai sanar da nadin sabbin kwamishinonin da za su maye gurbinsu.

Wani yanki na sanarwar na nuni da cewa, akwai yiwuwar sake nada wasu daga cikin mambobin majalisar.

Ya zuwa yanzu, gwamnan dai bai bayyana ainihin dalilin da yasa ya yanke shawarar korar kwamishinonin nasa ba.

An sha samun lokuta da dama da gwamnoni a Najeriya ke ruguza majalisar zartarwarsu saboda wadu dalilai da ba a rasa ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Damke Tukur Mamu, mai sulhu tsakanin yan bindiga da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna A Kasar Misra

Gwamna Ya Kori Kwamishinoninsa har 20 cikin 28 Daga Aiki

A wani labarin na daban, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a ranar Laraba da yamma, ya kori kwamishinoni 20 daga cikin kwamishinonin sa 28.

Kwamishinoni takwas da sanarwar ba ta shafa ba sun kasance daga ma'aikatun lafiya, matasa da wasanni, yawon bude ido, yada labarai da dabaru, al'amuran mata, ayyuka, kudi da fasaha.

Jaridar Punch a baya ta ruwaito cewa gwamnan yayi zargin makwanni biyu da suka gabata cewa wasu daga cikin wadanda ya nada suna zagon kasa ga gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.