N100,000 Nake Samu Idan Na Kai Harsasai 500: Matashin Mai Kaiwa 'Yan Bindiga Makamai Yayi Bayani
- 'Yan sandan jihar Niger sun cafke wani Umar Shehu mai shekaru 31 kan zargi samarwa da 'yan bindiga makamai
- Ya sanar da cewa, miyagun na biyansa N100,000 a duk harsasai 500 da ya kai musu wadanda yake samowa daga Taraba
- Ya tabbatar da ya shahara wurin kai malamai dajikan Madaki a Katsina, Maidoro a Kaduna da Kwamba Maje a Suleja
Niger - A kowanne harsasai 500 idan ya kai wa 'yan bindiga, ana biyansa N100,000 kamar yadda Umar Shehu matashi mai shekaru 31 ya sanar da 'yan sanda hedkwatar Minna a jihar Niger.
Shehu yace ya saba kai makamai ga 'yan bindiga a dajin Madaki dake jihar Katsina da dajin Maidoro na jihar Kaduna da kuma 'yan ta'addan Kwamba maje dake Suleja a jihar Niger.
Yace yana samo makaman ne daga wani Abdulmani a jihar taraba wanda jami'an tsaro suka kashe a Kaduna a farkon shekarar nan.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abiodun Wasiu yace an kama Shehu a Dikko Junction dake karamar hukumar Gurara a jihar Niger bayan bibiyarsa da aka yi, jaridar The Nation ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakazalika, 'yan sanda sun damke wasu mutum bakwai da suka hada da wanda ake zargi da kai wa 'yan bindiga bayanai mai suna Nasiru Musa dake da alaka da satar mutum hudu wanda aka halaka biyun a karamar hukumar Rafi ta jihar.
Jaridar Independent ta rahoto cewa, an yi garkuwa da mutun hudun a watan Nuwamban 2021 kuma aka shigar da su daji, Biyu daga ciki sun arce yayin da biyu aka kashe kashe su bayan karbar N13 miliyan na fansa.
Wasiu yace masu garkuwa da mutanen suna shirya yadda zasu sace shugaban karamar hukumar Rafi kafin a kama Shehu.
Kaduna: 'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 3 Dake Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanan Sirri
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna tace ta damke wasu mutum uku a Maraban Jos da Rigachikun a karamar hukumar Igabi ta jihar kan zarginsu da kai wa 'yan bindiga bayanan sirri.
Wadanda ake zargin an gano sunayensu da Hafsat Ibrahim, Rabi Bala da Bayero Adamu dukkansu matasa kuma sun shiga hannun 'yan sintirin jihar dake aiki a yankunan kwanaki biyu da suka gabata, sannan an mika su hannun 'yan sandan domin cigaba da bincike.
Daily Trust ta rahoto cewa, a yayin tabbatar da kamen, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, yace dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifukansu.
Asali: Legit.ng