2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF

2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF

  • Kungiyar dattawan yankin Neja Delta, PANDEF ta yi gargadin cewa ba za a samu matsala a Najeriya muddin mulkin ya cigaba da zama a arewa a 2023
  • Ken Robinsa, sakataren watsa labarai na PANDEF na kasa ne ya yi wannan gargadin a ranar Talata yayin ziyarar da ya kai wa Adewale Adebayo, dan takarar shugaban kasa na SDP
  • Kungiyar ta yi korafin cewa ana nuna wa yankin kudu wariya musamman wurin bada mukamai da morar arzikin kasa don haka idan ana son zaman lafiya ya kamata mulki ya koma kudu a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - A yayin da babban zaben 2023 ke karatowa, kungiyar dattawan yankin Neja Delta, PANDEF, ta ce akwai yiwuwar Najeriya za ta fuskanci matsaloli idan mulki ya tsaya a arewa, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

Sakataren watsa labarai na PANDEF, Ken Robinson ne ya furta hakan yayin ziyarar ban girma da suka kai wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP, Prince Adewale Adebayo a ranar Talata a Abuja.

Kungiyar Pandef
2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF. Hoto: @VangaurdNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na zuwa ne a yayin da PANDEF ke cewa za ta hada kan dukkan masu nufin Najeriya da alheri domin su bayyana rashin jin dadinsu game da rashin adalci da ake musu a kasar idan mulki ya koma a 2023.

Jawabin Ken Robinson, Sakataren Watsa Labarai na Pandef

Ya ce:

"Wannan ba barazana bane kuma ba wasa muke ba. Za mu hada kan mutanen mu a dazuka, gonaki da titunan Najeriya, da mutanen da ke tunanin yan Najeriya su yi aiki tare.
"Na fada a shirin talabijin cewa idan manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu suka tsayar da yan takara daga arewa, zai zama tamkar yaki ake yi da kudancin Najeriya. Muna wani yanayi da gwamnati ke nuna mana tamkar ba mu da rai a kasar."

Kara karanta wannan

2023: Shugaban CAN ya magantu kan abin da ya kamata fastoci su yi a lamarin jam'iyya

Ya cigaba da cewa:

"Muna cewa hakan ba adalci bane, kuma kowa ya ji. Za mu tafi kudu maso kudu, muna da abokai a jihohin tsakiyar Najeriya da arewa, za mu tuntubi dukkan yan Najeriya masu son ganin an yi adalci a arewa, saboda su sani cewa akwai bukatar mu yi aiki tare don kasar ta samu cigaba da bunkasa.
"Za mu yi magana da yan Najeriya kan dalilin da ya kamata shugaban kasa na gaba ya fito daga kudancin Najeriya; duk wani abin da ba wannan ba, ba muna fadan hakan a matsayin barazana bane amma Najeriya ba za ta cigaba da zama yadda ta ke ba idan mulki ya koma arewa a 2023."

Gwamnonin APC Na Arewa Sun Goyi Bayan Mulki Ya Koma Kudu, Sun Buƙaci Ƴan Takara Daga Arewa Su Janye

A wani rahoton, Gwamnonin jihohin arewa na jam'iyyar APC sun nuna goyon bayansu ga zaben dan kudu a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Gwamnonin sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar bayan wani taro da suka yi a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164