Hukumar EFCC Ta Kama Wani Mai Gidan Casu da Wasu 21 a Ibadan
- Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi nasarar cafke wasu mutane da zargin damfara
- An kwamushe wani mai gidan casu da ake zargin ya tara mutanen dake aikata dabi'ar damfara ta yanar gizo
- Hukumar EFCC na yawan kai samame wurare daban-daban a Najeriya tare da kame wadanda ake zargi da laifuka
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Oyo - Hukumar EFCC ta cafke wani Sunday Adepoju, mamallakin gidan kulob na De Rock dake Ibadan tare da wasu mutane 21 bisa zargin zamba ta yanar gizo.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a Ibadan a jiya Litinin 5 ga watan Satumba, Punch ta ruwaito.
A cewarsa, an cafke mutanen ne a gidan casun dake kan babbar titin Ring Road a birnin Ibadan a wani samame da jami’an leken asiri suka kai.
Hakazalika, ya ce an kama wasu ma'aurata; Aladenusi Ayodeji da Aladenusi Sadiat (da aka fi sani da Bonnie da Clyde).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wadanda aka kaman su ne; Ajuwon Ibrahim, Ogunniyi Stephen, Bolaji Quadri, Olajire Olamilekan, Ojo Kolapo, Kajero Sodiq, Kareem Abiodun, Bolaji Toheeb, Banjo Toyin da Clement Adeseye.
Hakazalika da Babalola Samuel da Opeyemi Omoyemi da Okesanya Matthew da Kareem Damilola da Aledegbe Qodir da Akindele Solomon da Adewopo John da Iyiola Ridwan da kuma Olabosinde Adesola da dai sauransu.
An kama matashi mai shekaru 36 da mota mai tsada
Ya kuma ce, an kama wani matashi mai shekaru 36 mai digiri a ilimin sinadarai da wata mota kirar Range Rover HSE kirar shekarar 2020, rahoton Premium Times.
Mista Uwujaren ya kara da cewa, an yi nasarar kame mutanen ne bayan dogon nazari da bincike da kuma samun bayanan sirri kan barnar da suka aikatawa.
Ya jero abubuwan da aka karba daga garesu da suka hada da motoci biyar, kwamfutar tafi-da-gidanka daya, wayoyin salula da wasu takardun bogi da ka iya kaiwa ga yaudara.
Karshe ya ce za a gurfanar da wadanda aka kwamushen a gaban kotu don fuskantar fushin hukuma..
Matashi Zai Yi Rayuwar Magarkama Bayan Sace Bindiga da Barkonon Tsohuwa a Ofishin ’Yan Sanda
A wani labarin, wata kotun Dei-Dei dake Abuja, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 21, Joshua Geoffrey, hukuncin daurin shekaru uku a magarkama, bayan kama shi da laifin satar bindiga da barkonon a ofishin jami’an ‘yan sanda.
An tuhumi Geoffrey dake zaune a Kubwa ta babban birnin tarayya Abuja da laifin babbar sata da ta saba doka, rahoton Daily Nigerian.
Geoffrey dai ya amsa laifinsa, inda ya fashe da kuka tare da neman afuwa da sassaucin alkali.
Asali: Legit.ng