Za a Zauna Cikin Duhu, Ma’aikatan Wutar Lantarki na Tunanin Komawa Yajin-Aikinsu

Za a Zauna Cikin Duhu, Ma’aikatan Wutar Lantarki na Tunanin Komawa Yajin-Aikinsu

  • ‘Yan Kungiyar ma'akatan wutar lantarki da na manyan ma'aikatan lantarki na kamfanonin Najeriya za su iya komawa yajin-aiki nan ba da dadewa ba
  • Dama tun farko ma’aikatan wutar lantarkin sun dakatar da yajin-aikinsu ne domin a samu damar da za a tattauna da kwamitin da gwamnati ta kafa
  • Yanzu maganar ta ki gaba-ta ki baya, ana zargin Hukumar kula da kadarorin gwamnati ba ta son biyan tsofaffin ma’aikatan PHCN kudin sallama daga aiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Makonni biyu bayan an samu shawo kan ma’aikatan wutar lantarki, labari ya zo cewa suna kokarin cigaba da yin yajin-aikinsu a fadin Najeriya.

Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba 2022 cewa ma’aikatan suna barazanar daina aiki ne saboda sabaninsu da gwamnati.

Korafin da ma’aikatan suke yi sun hada da rashin niyyar biyan tsofaffin ma’aikatan kamfanin wuta na Power Holding Company of Nigeria (PHCN) hakkokinsu.

Maganar hakkokin wadanda suka yi aiki a kamfanin PHCN da aka saida yana cikin abubuwan da suka jawo SSAEDC da NUEE suka tafi yajin-aiki kwanaki.

Jaridar tace jami’an hukumomin yaki da rashin gaskiya da almundahana, suna yi wa ma’aikatan lantarkin barazana a kan yarjejeniyar da aka yi da gwamnati.

Jami’an EFCC na kokarin tursasawa ma’aikatan wutan su amince da yarjejeniyar da aka yi tun lokacin da gwamnati ta saida lantarki ga ‘yan kasuwa a 2013.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lantarki
Tashar wutar lantarki Hoto: www.africanews.com
Asali: UGC

Kwamitin da aka kafa domin ya duba bukatun ‘ya ‘yan kungiyar na NUEE da SSAEDC ya yi zama a farkon makon nan, amma ba a iya cin ma matsaya ba.

Babban abin da ke kawo cikas shi ne batun hakkokin wadanda suka yi aiki da kamfanin PHCN, shekaru bayan korarsu daga aiki, ba a biya su kudin sallama ba.

Wata majiya tace hukumomi kamarsu BPE da ya kamata su dauki nauyin sallamar tsofaffin ma’aikatan, sam ba su da niyyar fito masu da hakkokin na su.

Babu mamaki a iya cin ma matsaya a wajen sauran batutuwa, amma lokaci ya kure ba tare da kwamitin ya iya tsaida magana game da kudin sallamar ba.

Ma’aikatan wutar lantarkin na reshen Legas da Ogun sun fitar da jawabi cewa sun shirya komawa yajin-aikin da zarar kungiya ta bada wannan sanarwa.

IPMAN sun shiga yajin-aiki

Kun ji labari dazu ‘yan kungiyar Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) sun fara yajin-aiki, sun ce gwamnati ta hana su kudinsu.

Masu dauko fetur daga Legas sun yi ikirarin suna bin hukumar NMDPRA bashin da ya taru tun daga farkon 2021 zuwa yanzu, sun ce kudin sun haura N50.6bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel