Alkali Ya Aika Matashi Gidan Yari Bayan Ya Watsawa 'Yar Sanda Najasa

Alkali Ya Aika Matashi Gidan Yari Bayan Ya Watsawa 'Yar Sanda Najasa

  • Alkali ta yankewa matashi mai shekaru 23 hukuncin zaman wata 6 a gidan yari tare da aiki mai tsananin wahala
  • Kamar yadda aka gano, matashin ya watsawa 'yar sanda kashi a jiki yayin da yake garkame a caji ofis kan cin zarafin wata tsohuwa
  • Alkalin ta bayyana cewa, damilare ba zai taba sauya hali ba saboda kwanakin baya an yanke masa hukuncin wata daya yana bautawa al'umma

Ibadan, Oyo - Wata kotun gargajiya mai daraja ta daya dake Ibadan jihar Oyo, a ranar Litinin ta yankewa matashi mai shekaru 23 mai suna Abayomi Damilare hukuncin zaman gidan maza na wata shida bayan ya watsawa ‘yar sanda kashi.

Alkalin kotun ta yankewa matashin wannan hukuncin bayan ya amsa laifinsa tare da shaidu gamsassu da aka mikawa kotun.

Kotun Gargajiya
Alkali Ya Aika Matashi Gidan Yari Bayan Ya Watsawa 'Yar Sanda Najasa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Akintayo a takaice ta yi shari’a tare da yankewa matashin hukuncin wata shida a gidan yari da aiki mai wahala.

Kara karanta wannan

Sam: Matashi ya tada kura yayin da yace ba zai ba da hayan matarsa a kan kudi N8.5bn

Alkalin ta kwatanta wanda ta yankewa hukuncin da mai laifin da ba zai taba tuba ba, Daily Nigerian ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda tace, wanda ta yankewa hukuncin an taba yanke masa hukuncin wata daya na bautawa al’umma kan wani mugun illa da yayi wa wani.

Tun farko, ‘dan sanda mai gabatar da kara, Sajan Ayodele Ayeni, ya sanar da kotun cewa tun a caji ofis aka kulle shi kan zargin cin zarafin wata tsohuwa.

Ayeni ya sanar da kotun cewa, Sajan Olofintuyi wacce ‘yar sanda ce ta hanzarta kai wa matashin dauki yayin da yake garkame.

Kamar yadda yace, yana son ganawa da ‘dan sandan dake binciken lamarin.

“Mai shari’a, Damilare ya dinga buga get din inda aka kulle shi yana son ganin IPO dake kula da lamarin yayin da Olofintuyi ta same shi.

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

“Sai dai Damilare ya watsa mata kashi tana bude inda yake kulle."

- Mai gabatar da kara yace.

Dan sandan ya mika hoton lokacin da cin zarafin ya faru da kuma takardar amsa laifinsa da yayi.

Ayeni yace laifin ya ci karo da sashi na 356 na laifukan jihar Oyo a Najeriya na 2000.

Bata Sallah kuma ta Tsani Mahaifiyata, Alkali Ka Taimaka Ka Raba mu, Magidanci ga Kotu

A wani labari na daban, wata kotu mai matsayi na farko dake yankin Kubwa ta babban birnin tarayya ta kashe aure mai shekaru 19 tsakanin 'dan kasuwa Lukman Abduaziz da matarsa Rashidat kan banbance-bancen da aka gaza shawo kansu.

Alkalin mai suna Muhammad Adamu, ya tsinke auren saboda Abdulaziz ya roki tabbatar da sakinsa kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Adamu wanda yace a Musulunci mutum yana da damar sakin matarsa yace Rashidat ta sanar da kotu cewa ta kammala iddarta.

Kara karanta wannan

Abin Al'ajabi: Halittar Wani Yaro Mai Shudin Ido Ya Girgiza Intanet, Jama'a Na Ta Cece-kuce Kan Bidiyonsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng