Zaman Lafiya A Kano: Ganduje Ya Fadi Babban Abin da Ya Sa Kano Ke Zaune Cikin Kwanciyar Hankali

Zaman Lafiya A Kano: Ganduje Ya Fadi Babban Abin da Ya Sa Kano Ke Zaune Cikin Kwanciyar Hankali

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da yasa suke zaune lafiya a jihar Kano, Arewa maso Yamma
  • Ganduje ya ce jihar sa tsira daga rikicin addini da na kabilanci ne saboda yadda ake mutunta juna da hakuri tsakanin mazauna
  • Sarkin Yarbawan Kano ya jinajinawa gwamnan sannan ya nemi a basu fili don su kafa sakatariyar kabilarsu a jihar

Kano - Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya danganta zaman lafiya da ake samu a jihar da mutuntawa da hakuri da ake yi tsakanin kabilu da addinai a jihar.

Ganduje ya kuma ce duk wasu kabilu da kungiyoyin addinai a kasar nan yan uwan juna ne, don haka akwai bukatar su rungumi zaman lafiya da hadin kai ba tare da la’akari da banbancinsu ba don samun ci gaba da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Ganduje ya fadi musabbabin zaman lafiya a Kano
Zaman Lafiya A Kano: Ganduje Ya Fadi Babban Abin da Ya Sa Kano Ke Zaune Cikin Kwanciyar Hankali | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana hakan ne a karshen mako a Kano yayin da yake jawabi a fadar sarkin Yarbawa na jihar, Daily Trust ta rahoto

An dai gudanar da wani biki ne a fadar sarkin Yarbawar don murnar sarautar da aka baiwa gwamnan da matarsa a kwanakin baya a masarautar Ibadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Yuni ne aka nadawa Ganduje da matarsa, Farfesa Hafsat Umar Ganduje sarautar Aare Fiwajoye da Yeye Aare Fiwajoye na kasar Ibadan.

Ganduje ya ce a shekarun baya, Kano ta yi fama da rikicin addinai da na kabilanci amma yanzu komai ya sauya saboda yadda ake nuna daidaito a tsakanin kabilu da addinai a jihar.

Ya kara da cewa dukkanin kabilu da ke zaune a jihar ana daukarsu ne a matsayin yan asalin jihar.

Jaridar ta nakalto Ganduje yana cewa:

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

“Ko da ake fuskantar matsalolin tsaro, muna tabbatar da ganin cewa mun ba cocinanmu kariya kamar yadda muke ba masallatanmu, saboda dukkanmu mutane ne kuma Allah ya yi mu daban-daban. Don haka ya zama dole mu gode ma Allah a kan haka, sannan mu rungumi junanmu don rayuwa a matsayin yan uwan juna.”

Sarkin Yarbawan Kano, Murtala Al’imash Otisese, ya ce bikin ya zama dole saboda sarautar ta dace da gwamnan da matarsa kuma ya cancanci karramawa.

Ya kuma bukaci gwamnan da bayar da fili don gina sakatariyar Yarbawa a jihar, wanda gwamnan ya yi alkawarin aikata hakan.

Shettima Ya Bayyana Babban Dalili 1 Da Yasa Dole Arewa Ta Goyi Bayan Tinubu

A wani labari na daban, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa lokaci ya yi da arewa zata saka waAsiwaju Bola Tinubu.

A cewar Shettima yanzu ne lokacin da arewa zata biya bashin gudunmawar siyasa da dan takarar shugaban kasar na APC ke ta ba yankin tsawon shekaru da dama.

Kara karanta wannan

Kano: Masu Fadi a Ji Sun Dira Auren Diyar Sarki Aminu Bayero da 'Dan Sarkin Kibiya

Da yake jawabi a yayin kaddamar da motocin kamfen din Tinubu/Shettima a ranar Asabar a Abuja, Shettima ya ce dan takarar shugaban kasar na APC ya sadaukar da komai nasa ga arewa, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel