Zaben Gwamnan Jihar Bauchi: Mutum 14 Dake Dakon Kujerar Kauran Bauchi

Zaben Gwamnan Jihar Bauchi: Mutum 14 Dake Dakon Kujerar Kauran Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed, zai fuskanci akalla mutum 15 masu neman tunbukeshi daga karagar mulki a 2023 kamar yadda ya yiwa magabacinsa, Mohammed Abubakar a 2019.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Al'ummar jihar Bauchi sun shahara da zabe ba tare da la'akari da jam'iyya ba, ana kyautata zaton hakan zai maimaitu a 2023.

A wani rahoton DailyTrust, an tattaro jerin mutum 14 dake son tunbuke Bala Mohammed daga mulki a 2023.

Bauchi
Zaben Gwamnan Jihar Bauchi: Mutum 14 Dake Dakon Kujerar Kauran Bauchi Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

Ga jerinsu:

1. Air Marshal Sadique Baba Abubakar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC)

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Sanata Halliru Dauda Jika na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP)

3. Hassan Khalid na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP)

4. Auwal Adamu jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM)

5. Abubakar Ibrahim na jam'iyyar Labour Party (LP)

6. Ahmed Magaji Saleh, na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP)

7. Umar Farouq Ahmed na jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP)

8. Saleh Auwalu Dahiru, na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC)

9. Mustapha Usman Dankyarana na jam'iyyar ADP

10. Musa A Magaji na jam'iyyar Action Alliance (AA)

11. Ahmed Magaji Saleh.

12. Saleh Sulaiman na jam'iyyar National Rescue Movement (NRM)

13. Kabiru Abdulhamid Shuwa na jam'iyyar Action Peoples’ Party (APP) da

14 Umar Garba Aliyu na jam'iyyar, Young Progressive Party (YPP).

Yayinda zaben ke gabatowa, ana hasashen mutum uku ne zasu takara rawar gani a zaben kuma daya cikinsu zai lashe.

Sun hada da Gwamna Bala Mohammed, Air Marshal Sadique Abubakar da kuma Halliru Dauda Jika na NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel