Yajin Aikin ASUU: Da Alamu Daliban Najeriya Za Su Koma Aji, SERAP Za Ta Maka Gwamnatin Buhari A Kotu
- SERAP ta sanar da cewa za ta kallubalanci gazawar da gwamnatin tarayya ta yi na biya wa ASUU bukatunta a yayin da yajin aikin ya shiga kwana 200
- Kungiyar mai fafutikar tabbatar da adalci a al'amuran mulki ta bukaci daliban Najeriya suma su yi karar gwamnatin tarayyar don tilasta mata biya wa ASUU bukatunsu
- A ranar 14 ga watan Fabrairu, ASUU ta fara yajin aikin gargadin na wata daya, wanda daga bisani ya kai har wata shida saboda rashin biya mata bukatunta
Kungiyar nan mai mai fafutikar tabbatar da adalci a al'amuran mulki (SERAP) ta ce tana shirya takardun shigar da kara kotu domin kallubalabtar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan rashin kawo karshen yajin aikin ASUU.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter, @SERAPNigeria.
Kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta fara yajin aikinta ne tun watan Fabrairu kuma yau Juma'a 2 ga watan Satumba ya shiga kwana 200.
Yanzu-Yanzu: Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Ɗaya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar 14 ga watan Fabrairu, kungiyar ta sanar da fara yajin aikin gargadi kan gazawar gwamnati wurin biya mata bukatunta da suka hada da allawus-allawus, biyan kudin inganta jami'o'i, aiwatar da tsarin biyan albashi na UTAS a maimakon IPPIS na gwamnati da wasu dalilan.
Amma SERAP, cikin sanarwar da ta fitar a sahihin shafinta na Twitter, ta ce za ta maka gwamnatin tarayya a kotu tunda ta gaza kyalle daliban Najeriya su koma makaranta.
Ta bukaci daliban na Najeriya su shigar da kara a kotun tare da ita.
SERAP ta ce:
"Muna shirya takardun kotu domin karar gwamnatin Buhari kan gazawarta na cika wa ASUU bukatunta don kyale daliban Najeriya su koma makaranta.
"Ka nuna sha'awarka na shigar da karar tare da mu musamman idan kai dalibi ne na jami'a."
Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki
A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda gwamnatinsa a cikin kwana daya ta magance yajin aikin wata hudu da kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta taba yi.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba wurin bikin cikar Bishop Mathew Kukah shekaru 70 da haihuwa da aka yi a Cibiyar Kukah da ke Abuja, Daily Trust ta rahoto.
Legit Hausa ta rahoto cewa jami'o'i a Najeriya sun fara yajin aiki tun watan Fabrairu kan rashin cika musu bukatunsu da gwamnatin tarayya ba ta yi ba.
Asali: Legit.ng