Ni Fa Ban Yarda Da Kudin Tallafi N6tr Da NNPC Tace Tana Biya Ba, Shugaban Kwastam Hameed Ali

Ni Fa Ban Yarda Da Kudin Tallafi N6tr Da NNPC Tace Tana Biya Ba, Shugaban Kwastam Hameed Ali

  • Gwamnatin tarayya na shirin cire tallafin man fetur bayan saukan shugaba Buhari a Yunin 2023
  • Idan aka cire tallafin man fetur, farashin litan mai na iya kaiwa N600 zuwa N800 a gidajen mai
  • Shugaban hukumar kwastam yace shi fa bai yarda akwai gaskiya cikin kudin da gwamnati ke cewa tana kashewa ba

Abuja - Kwantrola Janar na hukumar hana fasa kwabri watau Kwastam, Hameed Ali, a ranar Alhamis ya nuna rashin yardarsa da N6tr da gwamnati ke ikirarin ta kashe kan tallafin mai a 2022.

Hameed Ali ya bayyana hakan yayinda ya bayyana gaban kwamitin kudi na majalisar wakilan tarayya, rahoton Tribune.

Ya ce maganar cewa ana shan litan man fetur 98 a rana karya ne, lita milyan 38 fitar da shi ake kasashen waje.

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Matashi Dan Shekaru 15, Ya Ce Mawaki Davido Ba Zai Iya Siyan Irinsa Ba

Yace:

"Ni fa kullum ina gardama da NNPC. Idan muna shan litan mai milyan 60 kullum kamar yadda suka fada, ta wani dalili zasu rika fitar da milyan 98? Idan kun san adadin abinda muke sha, me yasa kuke fitar da fiye da hakan?."
"Tankokin mai nawa zasu iya daukar litan mai milyan 38? Wacce hanya suke bi su fita kuma ina suke kaiwa?"

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ta yaya suka gano lita milyan 60 ake sha a rana? Ni inda nike da matsala kenan. "
"A kimiyance, ba zai yiwu in cika tankin mota na yau ba, gobe kuma in sake cikawa."
Hameed Ali
Ni Fa Ban Yarda Da Kudin Tallafi N6tr Da NNPC Tace Tana Biya Ba, Shugaban Kwastam Hameed Ali
Asali: UGC

Zamu Karbi Sabon Bashin N11tr Kuma Zamu Sayar Da Wasu Dukiyoyin Gwamnati A Shekarar 2023, Minista Zainab

Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata karbi sabon bashin sama da N11 trillion tare da sayar da dukiyoyin gwamnati don kasafin kudin 2023.

Kara karanta wannan

Abin Al'ajabi: Halittar Wani Yaro Mai Shudin Ido Ya Girgiza Intanet, Jama'a Na Ta Cece-kuce Kan Bidiyonsa

Ta bayyana cewa gwamnati zata bukaci kudi N12.42 Trillion idan har zata cigaba da biyar tallafin mai a 2023.

Hajiya Zainab ta bayyana hakan ne ranar Litnin yayinda ta bayyana gaban yan majalsar wakilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel