Gwanonin Ribas da Imo sun yi fatali da batun kebe wuraren kiyo a jahohin su

Gwanonin Ribas da Imo sun yi fatali da batun kebe wuraren kiyo a jahohin su

Gwamnan jihar Imo dake a kudu maso gabashin Najeriya wata Rochas Okorocha da kuma ke zaman shugaban gwamnonin jam'iyya mai mulki ta APC ya bayyana shawarar kebe wuraren kiwo da za'ayiwa fulani makiyaya kamar yadda gwamnatin tarayya ta bukata a matsayin gurguwar shawara.

Hakama dai shima takwaran sa na jihar Ribas, Wike ya bayar da tabbacin cewa ba zai goyi bayan wannan yunkurin ba a jihar sa.

Gwanonin Ribas da Imo sun yi fatali da batun kebe wuraren kiyo a jahohin su
Gwanonin Ribas da Imo sun yi fatali da batun kebe wuraren kiyo a jahohin su

KU KARANTA: Ku bamu Sanata Shehu Sani idan ba ku so - Sanata Ben Bruce ga APC

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Sanatan dake wakiltar jihar Kaduna ta kudu a majalisar dattijan Najeriya watau Sanata Danjuma Laah a jiya Talata ya yi fatali da kiran gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari na kebe wuraren kiwo na musamman domin fulani a yankin.

Sai dai Sanatan ya bayyana cewa yankin da yake wakilta ko kusa ba za su taba amincewa da hakan ba domin kuwa dukkan kasar dake yankin su suna anfani da ita ne wajen noma kuma ba za su taba baiwa wasu bakin haure ba.

Legit.ng dai ta samu cewa a 'yan kwanakin nan dai an samu tashe-tashe hankula sosai musamman ma tsakanin manoma da makiyaya jahohin dake arewa ta tsakiyar Najeriya da kuma ma sauran sassan Najeriya batun da yayi matukar daukar hankalin 'yan Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng