Dabarar da Bankuna Suke Bi Domin Cin Riba Kan ‘Yan Najeriya Wajen Canjin Dala

Dabarar da Bankuna Suke Bi Domin Cin Riba Kan ‘Yan Najeriya Wajen Canjin Dala

  • A Yulin shekarar 2021, babban bankin kasa na CBN ya bada sanarwar dakatar da saida kudin kasashen waje ga ‘yan canji
  • Tun da CBN ya daina saida kudin ketare ga Bureau du Change, bankuna ke cin karensu babu babbaka wajen saida Dala
  • A maimakon Bankuna su saida Dala 1 a kan N414, mutane suna sayen Dalar Amurka $1 a kan N460 ko ma fiye da haka

Abuja - Tun shekarar bara, gwamnan babban banki na CBN ya bada umarni a daina saida Dala ga masu kasuwancin canji watau ‘yan Bureau du Change.

Rahoton Bussiness Report ya nuna cewa tun daga lokacin da aka bada wannan umarni, farashin Dalar Amurka ya cigaba da tashi a bankunan kasuwa.

Kara karanta wannan

"Wasu Tsaffin Janar-Janar Din Soja Sun Min Barazana Da CIA," In Ji Wike

A maimakon a ji bankuna sun saida Dalar a kan 414/$1 da CBN tsaida, suna cin riba fiye da kima.

Bankuna da-dama da ke Najeriya suna saidawa mutane Dala 1 a kan N460, a wasu lokutan, farashin da mutane ke sayen kowace Dala daya ya zarce haka.

A sanar da bankin CBN

Rahoton da muka samu ya nuna kazamar ribar da bankuna ke samu ya sa masana suna bada shawarar a kai korafi wajen babban bankin CBN na kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai sashe na musamman a karkashin CBN da ke da nauyin sa ido a harkar sauran bankuna.

Gwamnan CBN Hoto: guardian.ng
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Bambancin 45% a bankuna

Jaridar ta tattauna da mutanen da ke amfani da bankuna iri-iri, ta fahimci bambancin da ke tsakanin saye da saida Dalar Amurka ya kai 45.15%.

Sayen kudin kasar waje ya fi tsada a kan saidawa a bankuna. Yayin da bankuna suke sayen Dala a kan N410 daga CBN, suna cin ribar akalla N50 a duk $1.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

Yadda ake yi mana shigo-shigo babu zarfi

Wani mutumi ya shaidawa manema labarai yadda aka saida masa $1 a kan N601 a watan da ya wuce. A makon nan kuma ya saye $1 a kan N595.08.

Dabarar ita ce bankuna ba su fadawa mutum a kan nawa za a saida masa Dala. Sai an gama ciniki sai ya fahimci ya saye $1 ne a kan N50 zuwa N480.

Farashin bankuna

Ga yadda wasu bankuna suka saida $1, duk ya zarce farashin da aka yanke. Union Bank kadai aka samu sun saida N412/$ a daidai wannan lokaci.

Access Bank N450

UBA N465/$

Ecobank N450/$

Wema Bank N461/$

FCMB N480/$

Sterling Bank N460/$

Standard Chartered Bank N463/$

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng