Dan Allah Ki Kamani: Matashi Ya Rude Da Ganin Kyakkyawar Yar Sanda, Mutane Sun Rirrike Shi

Dan Allah Ki Kamani: Matashi Ya Rude Da Ganin Kyakkyawar Yar Sanda, Mutane Sun Rirrike Shi

  • Wani matashi a wajen shagalin bikin ‘Notting Hill’ a kasar Birtaniya ya bayyana yadda ya hadu da wata kyakkyawar yar sanda
  • A cikin wani bidiyo da ya wallafa a soshiyal midiya, mutumin na ta ihun neman jami’ar ta kama shi saboda tana da tsantsar kyau
  • Sai da abokan matashin suka janye shi daga wajen inda ya haddasa yar karamar dirama

Birtaniya - Wani matashi a kasar Birtaniya ya nadi wani bidiyo da ke nuna lokacin da ya hadu da wata kyakkyawr jami’ar yar sanda a wajen wani shagalin biki.

A cikin bidiyon, matashin yana ta ihun “ki kamani dan Allah”. Jami’ar yar sandan ta murmusa sakamakon yabon da take ta samu daga matashin dan farar hula.

Yar sanda da matashi
Dan Allah Ki Kamani: Matashi Ya Rude Da Ganin Kyakkyawar Yar Sanda, Mutane Sun Rirrike Shi Hoto: TikTok/@a20widahenney
Asali: UGC

An janye shi

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

Jim kadan bayan ya fara nadan bidiyon, ya nunawa mutane yadda jami’ar yar sandan ta yi kyakkyawan shiga mai daukar hankali wanda ya fito da tsantsar kyawunta. Matashiyar ta kasa daina yin dariya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake ci gaba da jinjinawa jami’ar tsaron da mika hannu wajenta, sai wani mutum ya rirrike shi sannan ya janye shi daga wajen.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

delsingh375 ya ce:

“tana da kyau tana iya kamani a kowace rana.”

korexforex ya ce:

“Kyawu na hakika!!!”

Kingdom ya ce:

“Na kusa karya kafana yayin da nake gudu zuwa bangaren sharhi.”

Fraser ya ce:

“tana iya sakani a kurkuku ba zan damu ba.”

Hotunan Kyawawan Yan Gida Daya Da Ke Aikin Yan Sanda Ya Gigita Samari

Kara karanta wannan

Abin Al'ajabi: Halittar Wani Yaro Mai Shudin Ido Ya Girgiza Intanet, Jama'a Na Ta Cece-kuce Kan Bidiyonsa

A wani labarin, wasu kyawawan yan mata yan gida daya wadanda ke aiki a matsayin jami’an yan sandan Najeriya sun yi fice bayan hadaddun hotunansu sun yadu a soshiyal midiya.

Karamar cikinsu ta je shafin TikTok don wallafa hotunan da suka dauka tare da yayar tata kala-kala, inda ta bayyana cewa tana matukar kewarta.

Hoton farko da ta daura ya nuno wasu kyawawan yan mata tsaye a gaban ofishin yan sanda cikin shigar yan sanda ta bakin kaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel