Dan Najeriya Da Baida Ilimin Boko Ya Kera Babura A Katsina, Hotunan Sun Haifar Da Martani

Dan Najeriya Da Baida Ilimin Boko Ya Kera Babura A Katsina, Hotunan Sun Haifar Da Martani

  • Wani mutumin Katsina mai suna Injiniya Kabir ya burge yan Najeriya da dama da fasaharsa ta kera babura
  • Hotunan baburan da Kabir ya kera sun karade shafukan soshiyal midiya inda ya sha jinjina daga yan Najeriya
  • Wasu sun yi kira ga gwamnati da ta taimaka mutumin da tallafin da zai dunga yinsu da yawa don siyarwa a kasuwa

Katsina - Wani dan Najeriya da aka bayyana a matsayin Injiniya Kabir ya burge mutane da dama da baiwarsa domin yana kera babura ne daga kayayyaki.

Wata wallafa da @yunusxonline yayi, ya bayyana cewa Injiniya Kabir wanda ke zama a Garejin Ali Chizo a jihar Katsina bai yi karatun boko ba.

Babura
Dan Najeriya Da Baida Ilimin Boko Ya Kera Babura A Katsina, Hotunan Sun Haifar Da Martani Hoto: Abdullahi Bambale
Asali: Facebook

An gano wata wallafa makamanciyar wannan a shafin Facebook din wani Abdullahi Banbale wanda ya watsa lambobin wayan Kabir (07063146240 da 08155894355) ga duk mai bukatar siyar haajarsa.

Kara karanta wannan

Idan Na Taba Satar Kudin Gwamnati, Allah Ya Tsine Mana Albarka, Peter Obi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan fasaha ta mutumin ya burge yan Najeriya da dama a soshiyal midiya inda suka jinjina masa.

Babatunde Matanmi ya ce:

"Hakan ya yi kyau kuma ya burge, sannu da kokari. Ina mai bayar da shawarar ya sanya mata suna Kabircycle."

Nnamdi God'SonsFinest Okafor ya ce:

"Abun burgewa, ina tankar mai? ku baya amfani da mai?"

Akinlolu Akinnifesi ya ce:

"Duba fa! Allah ya albarkaci aikin hannunsa."

Hotuna: Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30

A wani labarin, mun ji cewa kyawawan hotunan adaidaita sahu masu aiki da lantarki wanda kamfanin Phoenix Renewable Limited ya kera a Maiduguri sun yadu a shafukan soshiyal midiya.

Hadaddun hotunan adaidaita sahun wanda ake yiwa lakabi da Keke Napep ya sanya yan Najeriya da dama tofa albarkacin bakunansu sannan sun bukaci gwamnati da ta tallafawa kamfanin.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ɗan El-Rufai Ya Ce ASUU 'Bata Da Amfani', An Masa Zafafan Martani

Shugaban kamfanin da ya kera adaidaita sahun, Mustapha Gajibo ya shahara wajen yin ababen hawa masu aiki da lantarki wanda yawancinsu motocin bas-bas ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel