Shugaban NNPC Ya Sanar Da Lokacin Da Najeriya Za Ta Dena Siyo Mai Daga Kasashen Waje
- Mista Mele Kyari shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya ce Najeriya za ta dena siyo mai daga waje a cikin shekarar 2023
- Kyari ya bayyana hakan ne wurin wani taro da tawagar sadarwa ta fadar shugaban kasa ta shirya a Aso Rock Villa a ranar Talata
- Shugaban na NNPC ya ce ana kyautata zaton daga watan Yunin 2023 matatan Dangote za ta fara aiki kuma za ta rika samar da lita miliyan 50 na fetur sannan za a gyara sauran matatun Najeriya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya ce Najeriya za ta dena siyo man fetur daga kasashen waje lokacin da matatar Dangote ta fara aiki zuwa tsakiyar shekarar 2023.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wurin taron da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya karo na 49 a Villa, Abuja, The Cable ta rahoto.
Babban Magana: Masallatai Da Coci-Coci Suna Satar Ɗanyen Man Fetur A Najeriya, In Ji Shugaban NNPC, Kyari
Za mu dena siyo mai daga kasashen waje a tsakiyar shekarar 2023 - Shugaban NNPC
Kyari, ya ce za a samu karin man fetur da ake samarwa saboda sabon fasaha da ake amfani da shi, yana mai cewa hakan zai faru a tsakiyar 2023, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
"Man da za a rika samu daga matatan Dangote da wasu kananan matatun mai na jihohi zai sa a dena siyo man fetur daga kasashen waje.
"Ko da dukkan matatun mu hudu suna aiki a matakin 90% da aka kafa su. Litan man fetur miliyan 18 kawai za su iya samarwa. Hakan na nufin ko da dukkansu na aiki yau, akwai bukatar a siyo mai daga waje."
Sai NNPP ta ce ba ta so kafin matatar Dangote ta kai mai kasuwa - Kyari
Ya cigaba da cewa NNPC ce ke da hannun jari kashi 20 cikin 100 a Matatan Dangote don haka ita ce za a fara yi wa tayin fetur din, sai ta ce bata so za a kai kasuwa.
Kyari ya kara da cewa Matatan na Dangote za ta fara aiki a tsakiyar shekara mai zuwa, yana mai cewa za ta iya samar da lita miliyan 50 na man fetur wato PMS.
Kalamansa:
"Idan aka hada wannan da kuma dawo da matatun man mu na kasa zai sa babu bukatar a rika siyo man fetur daga kasashen waje. Ba za ka ga ana shigo da wani abu daga kasar waje ba a shekara mai zuwa."
Masallatai Da Coci-Coci Suna Satar Danyen Man Fetur A Najeriya, In Ji Shugaban NNPC, Kyari
A wani rahoton, Kamfanin NNPC, ta zargi jami'an gwamnati, malaman addini, hukumomin tsaro da ma wasu ma'aikatanta da hannu wurin satar danyen mai a kasar, The Punch ta rahoto.
Da ya ke magana a wurin taron tawagar shugaban kasa karo na 49 a gidan gwamnati a Abuja, Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce dukkan rukunin mutanen kasar na da hannu a laifin.
Asali: Legit.ng