An Gama Jiran Watanni, Muhammadu Buhari Ya Rattaba Hannu a Sababbin Dokoki 8

An Gama Jiran Watanni, Muhammadu Buhari Ya Rattaba Hannu a Sababbin Dokoki 8

  • A ranar Litinin, 29 ga watan Agusta 2022, muka ji Mai girma Muhammadu Buhari ya sa hannu a wasu kudirori takwas da yanzu sun zama dokokin kasa
  • Wani jawabi da aka ji daga bakin Hon. Nasir Illa ya tabbatar da cewa wadannan kudirorin da suka zo gaban Mai girma shugaban Najeriyan sun samu shiga
  • Nasir Illa shi ne mai taimakawa shugaban kasa Buhari wajen harkokin majalisar wakilan tarayya, tsohon ‘da majalisar ya karbi aikin Hon. Umar El-Yakub

Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran dokokin da aka kawo za su taimaka wajen inganta aikin jiragen sama tare da bunkasa ilmin saye da hada magunguna.

Wasu cikin kudirorin da aka sa hannu a kai sun fi watanni shida a kan teburin shugaban kasar.

Mai taimakawa shugaban kasa, Buhari Sallau, ya jero wadannan kudirori da yanzu sun zama doka. Ga su nan kamar yadda ya kawo su a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa

1. CIVIL AVIATION ACT, 2022

An shafe makamanciyar wannan doka da aka kafa a 2006 da sa ran wannan dokar za ta kawo gyare-gyare a harkar jiragen sama tare da tabbatar da tsaro.

2. NIGERIAN METEOROLOGICAL AGENCY (ESTABLISHMENT) ACT, 2022

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dokar ta soke takwararta da aka sani ta 2003, an ba NiMet damar bada lasisi wajen kafa duk wata tashar duba yanayi tare da bin dokokin ICAO, WMO da SARP.

3. PHARMACY COUNCIL OF NIGERIA (ESTABLISHMENT) ACT, 2022

Ita kuwa wannan sabuwar doka ta kawo sauyi kan yadda ake gudanar da harkar kwayoyi, sannan za ta gyara ilmi da koyin aikin saye ko hada kwayoyi.

Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

4. Counselling Practitioners Council of Nigeria, 2022

An kawo hukumar da za ta rika sa ido wajen sana’ar horas da mutane da kuma bada lasisin wannan aiki.

5. Nigerian Council for Management Development Act, 2022

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

Dokar nan tayi waje da dokar Nigerian Council for Management Development Act da dokar National Centre for Economic Management and Administration Act, sannan aka kafa hukumar Nigerian Council for Management Development Act, 2022.

6. National Institute Of Credit Administration (Establishment) Act, 2022

Da wannan sabuwar doka za a kula da sha’anin bashi a kasar nan, an kuma kawo sharudan shiga cikin kungiyar.

7. Chartered Institute Of Social Work Practitioners (Establishment) Act, 2022

Wata hukuma da aka shigo da ita a dokar kasa ita ce wannan domin masu neman zama ma’aikatan taimakawa jama’a.

8. Advertising Regulatory Council Of Nigeria Act, 2022

Ita kuwa wannan doka ta kafa kungiyar da ke kula da duk abin da ya shafi rajistan ma’aikatan da ke kula da tallace-tallace.

Satar Sani Abacha

Kun ji labari cewa sau biyar kasar Switzerland tana dawo Miliyoyin Dalolin ga gwamnatin Najeriya wanda ana zargin Janar Sani Abacha ya boye su.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari ya kaddamar da kwamitin da zai tallata Tinubu a Najeriya

Bayan hawan Muhammadu Buhari mulki, kasashen Amurka da Switzerland sun maido Dala miliyan 633 a cikin kudin da ake zargin badakalar Abacha ce

Asali: Legit.ng

Online view pixel